Gabon: Ana kan hanyar gwamnatin farar hula
November 15, 2024Tuni dai gwamnatin kasar ta wallafa da kuma ma fostoci da ke kiran 'yan kasar da su kada kuri'ar amincewa da sabon kundin tsarin mulkin. Kamar yadda aka gani a biranen kasar dama irin jawaban da takardun neman ra'ayin masu zabe. Juyin mulkin da aka yi a watan Augusta bara shi ne ya kawo karshen mulkin iyalan Bango na shekaru 55, wanda gwamnatin ke gudana karkashin jam'iyar GDP wacce ita ce jam'iyya daya tillo da ta rike mulki a Gabon. Don haka a ganin masharhanta kamar su Apoli Bertrand Kameni, wannan wani sabon babin ne ga kasar. "Gabon na ganin sauye-sauyen tarihi, idan muka yi misali da tarihin kasar na kusan rabin karni da ya gabata.”
Sabon kundin tsarin mulkin dai zai sauya daga tsarin fidda shugaban kasa ta hanyar majalisar dokoki izuwa wanda za a zabi shugaban kasa da mataimakinsa kai tsaye, wadanda dukkansu za su yi wa'adin shekaru bakawai na wa'adi- biyu. Ma'ana kuma hakan na nufin za a cire ofishin firaminista, sannan kundin tsarin mulkin ya bai wa shugaban kasa damar nada alkalan da sauran mukaman ma'aikatan shari'a da kuma ba shi karfin iya rusa majalisa. Alex Vines, masani ne da ke sashin Afirka a Chatham House. "Wannan hanya ce ta sauyin gwamnati inda za a koma gaba daya mulkin farar hula, kasancewar shugaban mulkin sojan shi ne mutum na gaba da zai tsaya takarar shugaban kasa. Ko da shi ke a gaskiyya shugaba Nguema da ke mulkin soja yana da farin jini tsakanin 'yan Gabon.”
Sabon kundin tsarin mulkin dai ya kumshi batutuwa da dama na sakarwa 'yan adawa mara, ko da shi ke yana dauke da wasu tarnaki a daya bangaren, misali a fili ya tilasta wa ko wanNe dan kasa shiga aikin soja a matsayin bautar kasa haka zalika ya haramta auren jinshi daya. Kimanin mutane 860,000 za su kada kuri'a daga mazabu 2,800 a zaben raba gardaman, wanda gwamnatin ta ce ta ware dalar Amirka miliyan 44 don gudanar da shi.