1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gabon ta shigar da kara kotun ICJ kan wani tsibiri mai fetur

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim MAB
October 3, 2024

Janar Oligui Nguema da ke mulkin soji a Gabon ya ce tsibiran biyu mallakin kasar ne, amma Equatorial Guinea ta yi watsi da wannan ikirari, inda ta ce ba shi da tushe a hukumance.

Janar Brice Oligui Nguema da ke mulkin soji a kasar Gabon
Janar Brice Oligui Nguema da ke mulkin soji a kasar GabonHoto: AFP/Getty Images

Gabon ta shigar da kara kotun duniya ta ICJ da ke birnin Hague, bayan ikirarin mallakar wasu tsibirai uku masu dinbin arzikin man fetur, tana mai cewar tun shekaru hamin da suka gabata ne aka warware takaddamar, tsakaninta da Equatorial Guinea, wato a shekarar 1974. Sai dai Equatorial Guinea ta yi watsi da wannan ikirari na Gabon, inda ta ce ba shi da tushe a hukumance.

Takaddamar ta samo asali ne tun sama da shekaru 120 da suka gabata, lokacin da 'yan mulkin mallaka wato Faransa da Spain suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar ikon tsibiran, wadanda ke da arzikin man fetur da iskar gas.