1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaddhafi ya yi Allah wadai da NATO

April 30, 2011

Gaddhafi ya sake yin jawabin nuna bijirewar sa ga buƙatun ƙasashen Yamma da kuma 'yan tawayen Libiya

Shugaba Gaddhafi na LibyaHoto: Libya State Television via APTN/AP/dapd

Da sanyin safiyar wannan Asabar ce shugaban Libiya Muammar Gaddhafi ya fito ta tashar telebijin a ƙasar, inda yayi alƙawarin cewar ko ana ha-maza, ha-mata ba zai fice daga ƙasar ba, kuma ba zai taɓa miƙa wuya ba, ko da shike kuma ya ce ƙofar sa a buɗe take domin tattaunawa da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO. Ya ce a shirye dakarun sa suke su amince da yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta, amma ba wadda ya kwatanta da cewar ta nuna goyon baya ga ɓangare guda ba. A lokacin jawabin nasa kuma, shugaba Gaddhafi ya dasa ayar tambaya akan halaccin tsunduma cikin rikicin ƙasar sa da ƙungiyar ƙawancen tsaron NATO ta yi.

A halin da ake ciki kuma, an ci gaba da gwabza mummunan faɗa a ciki da kewayen birnin Misrata na ƙasar Libiya - mai tashar teku. A yammacin Jumma'a dai gwamnatin Libiya ta sanar da cewar tuni ta karɓe iko da tashar tekun dake birnin, amma ƙungiyar NATO ta ƙaryata batun. Hakanan ƙungiyar ƙawancen tsaron ta ce ta hana dakarun dake biyayya ga shugaba Gaddhafi sanya nakiyoyi a tashar tekun, inda suke bayyana cewar sun so ne su janyo matsala ga aikin kaiwa mabuƙata agaji a birnin Misrata da ake yiwa ƙawanya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita: Halima Balaraba Abbas