1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gadhafi ya ce yana nan daram a cikin Libiya

September 8, 2011

Shugaba Gadhafi na Libiya ya bayyana rahotannin ficewar sa daga ƙasar a matsayin farfagandar yaƙi

Moammar GadhafiHoto: AP

Hamɓararren shugaban Libiya Mouamer Gadhafi ya yi watsi da rahotannin da ke cewar ya tsere zuwa ƙasar Nijer dake makwabtaka da Libiya. A cikin wani saƙon sa da aka yayata ta wata tashar telebijin a ƙasar Siriya, Gadhafi ya kwatanta rahotanin da cewar farfagandan yaƙi ne kawai da kuma ƙarairayi. Hakanan ya yi iƙirarin cewar hatta jerin gwanon motocin sojin da aka gani sun isa jamhuriyyar Nijer, ba su ne ayari na farko ba.

Dama dai kakakin shugaban na Libiya ya jaddada cewar Gadhafi yana ci gaba da zama ne a cikin Libiya kuma cikin ƙoshin lafiya. Ba a dai san maɓoyar Gadhafi ba tun bayan da 'yan tawaye suka karɓe iko da birnin Tripoli - a ƙarshen watan daya gabata. A halin da ake ciki kuma, sabbin shugabannin Libiya suna shirin tinkarar yiwuwar gwabzawa da magoya bayan Gadhafi a birnin Bani Walid, wanda ke hannun dakarun dake biyayya ga hamɓararren shugaban har ya zuwa wannan lokaci.

Tuni mai shiga tsakani a ɓangaren 'yan tawayen na Libiya Abdallah Kenschil ya bayyana cewar akwai yiwuwar ɗan shugaba Gadhafi yana cikin birnin na Bani Walid:

" Ya ce Saif al-Islam ya koma birnin kuma an yi tozali da shi a jiya. Hakanan akwai jigo a cikin gwamnatin wanda bamu sanshi ba ciki kuwa harda Moussa Ibrahim."

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal