1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gagarumin aikin raya Afirka daga Jamus

November 11, 2016

Ministan raya kasa na Jamus Gerd Müller ya ba da shawarar kirkiro da wani gagarumin shirin habaka nahiyar Afirka tamkar "Marshall Plan" wanda zai matukar kara yawan tallafin da Jamus ke bai wa nahiyar ta Afirka.

Gerd Müller in Tansania
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Heimken

A wannan Jumma'ar dai wasu cibiyoyin nazarin tattalin arziki guda biyu sun gabatar da shawawarinsu game da wannan shiri ga ministan a birnin Berlin. Sai dai har yanzu da akwai ayar tambaya game da shirin.

Nazarin wanda cibiyar Club of Rome da kuma majalisar nazarin tattalin arziki suka yi dai, ya yi kira da a kirkiro wani babban asusu na kudi Euro miliyan dubu biyu don bunkasa tattalin arziki a Afirka da samar da wadata ga al'ummar nahiyar da ke kara yawa da kuma kirkiro aikin yi ga matasanta.

A lokacin gabatar da sakamakon nazarin ga ministan hadin kan tattalin arziki da raya kasa na Jamus, Gerd Müller, a birnin Berlin a wannan Jumma'a, shugaban majalisar nazarin tattalin Franz Josef Radermacher ya ce yanzu haka Jamus na kashe kwatankwacin Euro biyu ga kowane mutum guda a Afirka a fannin raya kasa.

Shugaba Issoufou ya taba neman wannan bukata ta "Marshall Plan" a wurin Merkel Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

 "Mun bada shawarar kirkiro da wani asusun bunkasa nahiyar Afirka, da gwamnatin Jamus za ta bada garanti ga masu zuba jari. Za a iya tara kudaden asusun a kasuwannin hada-hadar hannayen jari. Idan aka yi amfani da asusun da basira musamman wajen inganta hanyoyin sarrafa tattalin arziki da fannin masana'antu, to ke nan an ninka har sau biyu taimakon samar da wadata."

Nazarin ya kuma jaddada dinbim arzikin Afirka musamman a fannin noma da sabunta makashi, a saboda haka masanan suka yi kira da gina tashoshin samar da makamashi ta amfani da hasken rana a sassa dabam-dabam na Afirka a wani mataki na kirkiro da aikin yi da kuma magance matsalolin rashin isasshen hasken wutar lantarki a nahiyar. Masanan sun kuma yi kira da fadada ayyukan jin kai ga 'yan gudun hijira da wadanda aka tilasta musu barin yankunansu.

Ministan raya kasa na Jamus Gerd Müller ya sha nanata ra'ayin kirkiro da shirin "Marshall Plan" don rage matsalar talauci a Afirka.

Shi dai "Marshall Plan" asali wani shiri ne da Amirka ta kirkiro don farfado da tattalin arzikin yammacin Turai da ya ruguje bayan yakin duniya na biyu.

Gerd Müller a ziyararsa birnin KigaliHoto: picture-alliance/dpa/Phototek/U. Grabowsky

Saboda haka samar da wani shiri shigen "Marshall Plan" ga nahiyar Afirka alhaki ne a kan kasashe masu arziki, inji Minista Müller lokacin gabatar da sakamakon nazarin.

 "Dole mu zuba jari a wadannan kasashe, dole ne mu ba wa mutane wata kyakkyawar makomar rayuwa, idan ba haka ba to a cikin shekaru masu zuwa miliyoyin 'yan nahiyar ne musamman matasa da ba su da aikin yi, ba su kuma hango wata makoma a Afirka ba za su doshi hanyar zuwa Turai gudun hijira."

 

Ministan ya ce shirin ba zai zama wani sabon tsarin raya kasa da aka shirya a kasashen yamma ba  ba tare da la'akari da bukatu da kuma muradun Afirka.

Duk da alkawarin da ministan ya yi na gabatar da shirinsa na "Marshall Plan" ga Afirka nan ba da dadewa ba, abin da bai bayyana ba shi ne ko shirin zai tabbata, domin a lokacin ziyarar da ta kai Jamhuriyar Nijar, shugabar gwamnatin Angela Merkel ta ki ra'ayin na "Marshall Plan" inda ta fada wa Shugaba Mahamadou Issoufou cewa yanayin da ake ciki a Afirka sun bambamta gaba daya da wadanda Turai ta samu kanta ciki bayan yakin duniya na biyu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani