Gambiya: Barrow ya shekara kan mulki
February 19, 2018Shekara guda da shugaba Barrow ya yi, ta kasance mai cike da nasarori musamman wurin dabbaka 'yancin dan Adam. Wadanda ke yabawa gwamnatinsa na ganin kasar ta sake kulla dangantaka da kotun kasa da kasa mai hukunta masu manyan laifuka ta ICC da kuma kungiyar kasashe rainon Ingila, watau Common Wealth. A cewar shugaba Barrow, jama'ar kasar Gambiya sun san gwamnati ta ba su damar fadin albarkacin bakinsu inda yake cewa: " Mun cimma nasarar murkushe mulkin danniya. Yanzu mun mayar da hankali wurin ci gaba da dorewar salon mulkin demokaradiyya. Wannan kuma na bukatar hakuri da hadin kai tsakanin 'yan kasa. Mun san cewa za mu iya yin kuskure, amma za mu gyara a duk lokacin da muka fahimci mun kauce hanya. Burin mu dai shi ne ci gaba da gina sabuwar kasar Gambiya."
To sai dai yayin da shugaba Adama Barrow ke bugon kirji da irin ci-gaban da kasar ta samu wurin bada damar fadin albarkacin baki da ci gaba da bude sabon babi mai kyau a tarihin kasar, wasu 'yan kasar na ganin har yanzu ba su gani a kasa ba. Masu irin wanann ra'ayin, na kuka da yadda matsalar rashin aikin yi ke ci gaba da kasaita a tsakanin jama'a. Ga kuma yadda daukewar wutar lantarki ta zama ruwan dare a kasar ta Gambiya. Masu sukar gwamnatin ta Barrow, na ganin shugaban ya na "jan-kafa" wurin magance matsalar tattalin arziki da zamantakewa a kasar su na masu cewa: " Ya kamata shugaba Barrow ya inganta tattalin arzikin kasar mu. Duk da cewa an samu raguwar kudin sufuri a Gambiya, amma fa farashin kayayyaki a kasuwanni na kokarin wuce karfin talaka. Ya kuma kamata ya ba da karfi sosai wurin samar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a. "Ni na gamsu cewa wannan sabuwar gwamnatin ta Adama Barrow za ta ci gaba da ba kowa dama ba tare da tsangwama ba."
Shugaba Adama Barrow ya hau kan kujerar shuganci kasar Gambia ne bayan da ya lashe zaben da gagarumin rinjaye, inda ya kada tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh. A karon farko, Jammeh ya amince ya sha kaye a zaben, amma daga baya kuma ya yi amai ya lashe ta hanyar kin yarda da sakamkon zaben. Abin da ya sa aka yi ta kai ruwa rana kafin ya sauka daga kan kujerar mulki inda daga bisani ya fice daga kasar a matsayin mai neman mafakar siyasa.