Gambiya: Shugabannin Afirka na shirin halartar biki
January 12, 2017Talla
Shugaban na Benin da ke wata ziyara a kasar Cote d'Ivoir, ya ce su na masu nuna farin cikinsu ga jin wasu kalamman shugaba Jammeh da ke nunin cewa, yana fatan ganin an samun mafita a wannan rikici. A wani jawabi da ya yi ta kafoyin yada labarai na kasar, Shugaba Yahya Jammeh ya soki shishigin da ya ce wasu kasashe na yi wa batun kasar ta Gambiya, inda kuma ya yi fatan ganin an walwale wannan rikici ta hanyar ruwan sanyi.
A Laraba ce dai ta kamata tawagar kungiyar ECOWAS a kalkashin jagorancin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ziyarci birnin na Banjul domin tattaunawa da Shugaba Jammeh, amma kuma aka mayar da wannan tattaunawa ya zuwa ran Juma'a 13 ga wannan wata na Janairu.