1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gambiya ta dora buri kan zaben majalisa

April 4, 2017

A ranar Alhamis ne za'a gudanar da zaben 'yan majalisun dokokin Gambiya a karon farko tun bayan karshen mulkin shugaba Yahya Jammeh, inda 'yan kasar ke fatan zaben zai kawo wa kasar sauyi.

Senegal Proteste gegen Nicht-Anerkennung der Wahl in Gambia
Hoto: Getty images/AFP/Seyllou

'Yan takara 239 ne suke karawa tsakaninsu don neman lashe kujeru 48 a zaben majalisar dokokin kasar Gambiya. Shi kuwa shugaban kasa ya na 'yanci nada 'yan majalisa biyar; a takaice dai ana da kujeru 53 ne a cikin majalisar dokokin kasar da ke a yankin Afrika ta yamma. Akalla mutane 886,000 ne su ka yi rejista don kada kuri'unsu a cewar hukumar zabe mai zaman kan ta IEC.

Sai dai  al'ummar kasar Gambiya sun koka da mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh, wanda ya yi mulki na tsawon shekaru 22 inda ya sauya dokokin zartaswa daga wajen 'yan majalisa a lokuta da dama. Suna ganin cewar zaben majalisar zata kawo sauyi wajen gudanar da aiki cikin gwamnatin kamar yanda Musa faya wani mazaunin Banjul ke ce wa. "Abubuwa za su canja matuka, domin ko a siyasance,yanzu mutane na da damar yin takara, kuma akwai 'yan takara masu zaman kansu, don haka kana da zabin wanda kake so."              

Shugaba Barrow na fatan samun rinjaye a majalisar GambiyaHoto: Reuters/T. Gouegnon

Fagen Siyasar kasar Gambiya ya bada mamaki a 2012 lokacin da jam'iyar APRC ta Jammeh ta samu kujeru 43, sakamakon gibi da a ka samu na 'yan takara ta dalilin hamayya ta 'yan adawa. Wannan ne ma ya sa ba su da ikon tsoma baki a cikin al'umuran da suka shafi kasar. Yawancin 'yan kasar na kyautata zaton sabon tsarin mulkin kasar zai samar da ci gaba.  Kebba Bojang na daya daga cikin wadanda suka bayyana bukatun su kan sabon gwamnati. Ya ce "Ina so gwamnati ta lura da kudaden haraji, ta yi amfani da kudaden saboda masu zuba jari su shigo".