1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Fafutikar hukunta tsohon shugaban Gambiya Yahya Jammeh

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
October 16, 2021

Daruruwan mutane a binrin Banjul na Gambiya sun gudanar da zanga-zangar lumana, don neman ganin an hukunta cin zarafin bani Adama da tsohuwar gwamnatin Yahya Jammeh ta aikata.

Gambia Protest gegen Präsident Adama Barrow, Rücktrittsforderung
Hoto: DW/O. Wally

Masu zanga-zangar a Banjul babban birnin kasar Gambiya sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta cika alkawarin da ma'aikatar shari'a ta dauka na zartar da hukunci kan binciken cin zarafin bani Adama da wani kwamiti ya yi na tsawon shekaru biyu a yayin mulkin tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh.

Yahya Jammeh da yanzu haka ke gudun hijira sakamakon matsin lambar kungiyar ECOWAS, na da karfin fada a ji a cikin gida musamman ma a fagen siyasa. A baya-bayan nan ma an ambaci jam'iyyarsa da kulla kawance da ta Shugaba Adama Barrow da ke kan mulki, da niyyar tunkarar zaben shugaban kasa.