Ganawa tsakanin Masar da Turai
October 22, 2025
Ana ganawa ta farko tsakanin kasar Masar da kungiyar Tarayyar Turai inda shugabanni daga bangarorin biyu za su gana kan batutuwan tsaro da cinikayya gamida masu hijira, har da batun yankin zirin Gaza na Falasdinu.
Shugaba Abdel-Fattah el-Sissi na kasar ta Masar yana ganawar a birnin Brussels na Belgiyam tare da shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen gami da shugaban gudanarwar hukumar António Costa. Akwai kuma batun yankin zirin Gaza na Falasdinu da aka smau yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mayakan Hamas da gwamnatin Isra'ila.
Kungiyar Tarayyar Turai ta fi karkata ga Masar don samun gozon bayan cimma wannan aiki, sai dai kuma Turai ta dade tana sukar matakin Shugaba al-Sisi kann ctake hakkin bil Adama tun bayan abin da suka kira kwace mulki da karfi a 2013. Paul Taylor babban jami’i ne na cibiyar tsara manufofin EU.
Ana sa ran ganawar da janyo a kara yawan taimakaon tattalin arzikin da Masar take samu daga kungiyar Tarayyar Turai.