Ganawa tsakanin Merkel da Jetou
March 7, 2006To ko da yake wadannan batutuwan sune suka fi daukar hankalin jami’an siyasar biyu a lokacin ganawar tasu a birnin Berlin kamar yadda Angela Merkel ta nunar, inda ta ce dukkansu biyu sun bayyana sha’awar ganin an samu bakin zaren warware matsalolin dake akwai ko akalla samun ci gaba akan manufa, amma P/M kasar Maroko Driss Jettou yayi amfani da wannan dama domin yin kira ga neman hanyoyin shawo kann rikicin nan na yankin yammacin Sahara da aka yi shekara da shekaru ana fama da shi tsakanin Moroko da kungiyar fafutukar neman ‚yancin kann al’umar Saharawi ta Polisario a cikin ruwan sanyi. Ya ce wajibi ne a cimma wata manufa ta sulhu da zata samu karbuwa daga dukkan bangarorin da lamarin ya shafa tare da ikon cin gashin kann al’umar Saharawi karkashin wata hadaddiyar kasa ta Maroko. A lokacin da yake amsa tambayar da wakilin Deutsche Welle ya gabatar masa a game da matakin da kasar Maroko take neman dauka domin shawo kann rikicin na yankin yammacin Sahara a cikin gaggawa, P/M Dris Jettou cewa yayi, kasar Maroko dai tana sha’awar kyautata dangantakarta da dukkan kasashen dake makobtaka da ita, musamman ma kasar Aljeriya, amma tana kann bakanta na kafa babbar daular Maroko saboda a ganinta ta haka ne kawai za a samu kafar shawo kann matsaloli masu tarin yawa da suka yi wa yankin arewacin Afurka katutu.
Dris Jettou ya kara da cewar:
Kasar Maroko na hadin kai da kwamitin sulhu na majalisar dikin duniya da da ita kanta majalisar da kuma sakatare-janar dinta Kofi Annan da wakilansa domin neman hanyoyin magance rikicin dake akwai tare da tabbatar da hadin kann kasar. Mun gabatar da shawarwari masu yawa kuma muna ba da goyan baya ga manufar warware rikicin a siyasance, wanda ya tanadi ikon cin gashin kann al’umar Sharawi a karkashin wata hadaddiyar kasa ta Maroko.
A nata bangaren shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tayi nuni da irin rawar da Maroko ke takawa a tsakanin kasashen dake gabar tekun bahar-rum a karkashin yarjejeniyar nan da aka kira wai ta Barcelona. Merkel ta kara da cewar:
Mun tattauna akan yarjejeniyar nan ta Barcelona Kuma Jamus zata ba da gudummawarta lokacin da zata karbi ragamar shugabancin Kungiyar Tarayyar Turai. Kuma a nan wajibi ne in yaba wa kasar Maroko a game da rawar da take takawa da kuma hadin kann da take ba wa makobtanta, wanda ka iya zama abin koyi ga sauran kasashe.
A dai halin da ake ciki yanzu kamar yadda Merkel ta nunar kasar Maroko na daya daga cikin kasashen da suka fi cin gajiyar taimakon da Kungiyar tarayyar turai ke bayarwa, kuma ba shakka zata samu karin taimakon in har ta samu ci gaba a shirye-shiryenta na raya kasa. A baya ga batutuwan na zanen batanci da matsaloli na yankin gabas ta tsakiya, Merkel ta ce sun yi musayar yawu akan shawarwari na siyasa da musayar al’adu da sauran dangantaku na kasa da kasa.