1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawa Tsakanin Schröder Da Blair

July 15, 2004

A yau alhamis shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder ya sadu da takwaransa Tony Blair a birnin London

Schröder da Blair na ban kwana a Downing Street
Schröder da Blair na ban kwana a Downing StreetHoto: AP

Schröder, wanda tun da farkon fari ya fito fili ya bayyana kyamar kai wa kasar Iraki hari domin hambarar da gwamnatin shugaba Saddam hussein a cikin watan maris na shekarar da ta wuce ya kai ziyarar tasa ga Birtaniya ne a daidai wannan makon da aka kwatanta tamkar mafi tsauri ga P/M Tony Blair tun bayan da ya dare kan karagar mulkin Birtaniya. To sai dai kuma rahotannin da aka dade ana sa ran samunsa daga kwamitin bin bahasin da aka nada domin binciko rawar da hukumar leken asirin Birtaniya ta taka dangane da zargin Iraki da mallakar makaman kare dangi da na guba, wanda aka gabatar a jiya laraba, ya yi nuni da cewar Birtaniya ta ba wa Amurka hadin kai ne bisa wasu hujjojin da basu da tushe, ko da yake shi kansa Blair ba ya da laifi a game da wannan kuskure da aka caba. Ko da yake maganar Irakin na daya daga cikin batutuwan da ake kyautata zaton shuagabannin biyu sun tattauna kansu, amma sun fi mayar da hankali ne akan batutuwan da suka shafi Kungiyar Tarayyar Turai. Jim kadan bayan ganawar Schröder ya bayyanar a fili cewar Jamus ba zata kada kuri’ar raba gardama akan daftarin tsarin mulki bai daya na kasashen Turai da aka cimma daidaituwa kansa kwanan baya ba, bisa sabanin kasar Faransa, wacce a jiya laraba shugabanta Jacques Chirac ya ba da sanarwar cewa al’umar kasar ne zasu yanke shawara a game da makomar daftarin tsarin mulkin na kasashen Turai. Kazalika Schröder yayi fatali da tambayoyin da aka gabatar masa a game da wanzuwar baraka a dangantakar Jamus da Birtaniya. Shugaban gwamnatin na Jamus ya ce sun yi shawarwari masu ma’ana a karkashin wani kyakkyawan yanayi kamar yadda aka saba a zamanin baya. Ba shakka an samu sabanin ra’ayi a tsakanin illahirin kasashen KTT a taron kolin da suka yi a karshen watan da ya gabata dangane da maganar magajin Romano Prodi, inda daga baya suka dace akan Jose Manuel Barroso dan kasar Portugal domin shugabancin hukumar zartaswa ta KTT, in ji Schröder a daidai lokacin da suke masafaha ta ban kwana da Tony Blair a kofar fadarsa ta Downing Street bayan ganawa ta tsawon awa guda.