Ganawar Jonathan da iyayen 'yan Chibok
July 22, 2014Ganawar da ke zaman irinta ta farko da kuma ke zuwa kwanaki kusan 100 da satar 'ya'yan nasu dai, na zaman sabon fata ga Abujar na rage radadin sukar da ke zaman ruwan dare gama duniya a halin yanzu.
Duk da sabon alkawarin ceto musu 'ya'yan cikin kankanen lokacin da ke tafe, ganawar dai ta zamo kafa na nuna bacin ran iyaye kusan 160 da suka samu halartar zauren, kuma suka ce suna zaman jiran gani a kasa na alkawura na sake kyautata tsaro da ma ilimi a cikin yankin da daga dukkan alamu al'amurransa ke kara nuna alamar lalacewa.
Malam Muhammad dai na zaman daya a cikin iyayen yaran kuma a fadarsa ta karatu na karen da ake biki tsakiyar gidansu ne kawai ke zaman makoma a gare su ga kokarin tabattar da komawa dai dai a cikin yankin.
" Yayi mana alkawari dama shi ne muke fatan samu, Allah dai da ikonsa ya taimaka ya sa karfi Allah ya sa mu same su. Ya ce zamu hada kai da gwamnatin Borno dama mun rasa tsaro ne in akwai tsaro duk inda suke za'a je. Abun da ya bayyana mana ke nan ragowar kuma sai mun gani".
To sai dai koma ya zuwa yaushe ne dai alkawarin ta kusan isan ke shirin tabbata ga iyayen dama yan matan da 53 a cikin su suka zo ga Abujar domin sauraren shugaban kasar ke shiri na tabbata dai, ko bayan rashin tsaron taron na Abuja ya kuma dubi batun yiwuwar komawar 'yan makaranta a bangaren 'ya'yan na Chibok da ma ragowar 'yan uwansu da ke Borno da kuma yanzu haka ke gida suna hutun dole.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar