Ganawar MDD da hukumomin Koriya ta Arewa
December 9, 2017A karon farko jami'an MDD sun gana da hukumomin Koriya ta Arewa bayan shekaru masu yawa. Jeffrey Feltman babban jami'in MDD ya kammala ziyarar kwananki biyar a Pyongyang, inda a yanzu ya isa Beijin babban birnin kasar China. A ganawar ta su Koriya ta Arewa ta zargi Amirka da haddasa zaman dar-dar a yankin. Amma duk da haka dai hukumomin Pyongyang sun yi alkawari ci gaba da tuntuba tsakanins da MDD. Ziyarar ta zo ne mako guda bayan da Koriya ta Arewa ta harba wani makamin linzami, wanda kan iya kai wa ga ko'ina na cikin kasar Amirka. A yayin ziyarar dai Jeffrey Feltman, ya gana da ministan harkokin waje Ri Yong-Ho da kuma karamin ministan harkokin waje Pak Myong-Kuk. Wannan shi ne karon farko da wani jami'in MDD ya ziyarci Koriya ta Arewa tun shekara ta 2010