1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahmoud Abbas ya kai ziyara yankin Yahudawa

Ramatu Garba Baba
December 29, 2021

A karon farko cikin shekaru fiye da goma da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ke kai ziyara Isra'ila, inda ya gana da ministan tsaron Isra'ila Benny Gantz.

Benny Gantz und  Mahmoud Abbas
Hoto: picture alliance/REUTERS

Shugaban Gwamnatin Falasdinawa Mahmoud Abbas ya gana da ministan tsaron Yahudawa Benny Gantz, a wata ziyarar ta ba-zata da ta shiga kundin tarihi, inda majiyar ma'aikatar tsaron Isra'ila ta ce, sun tattauna batutuwan da suka danganci tsaro da yadda za a inganta zamantakewa a tsakanin kasashen biyu. Ziyarar na daya daga cikin jerin ganawar da manyan jami'an Isra'ilan ke yi da jagoran Falasdinawan a baya-bayan nan.

Duk da cewa sabon firaiministan Isra'ila Naftali Bennett, ya riga ya kawar da batun tattaunawar zaman lafiya a tsakaninsu bisa kin amincewa da 'yancin gashin kan makwabtansa, ya ce, yana son ganin an shawo kan takun saka da Falasdinawa tare da inganta yanayin rayuwar al’ummar da ke zaune a yankin yammancin Kogin Jordan da Isra’ilan ta mamaye.