1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gangamin adawa a dandalin Tahrir na Masar

Zainab MohammedJune 5, 2012

Dubban al'ummar Masar ne ke ci gaba da gudanar da gangamin adawa a dandalin Tahrir dangane da sassaucin hukuncin da aka yanke wa tsohon shugaba Hosni Mubarak da mukarrabansa.

Presidential candidate Hamdeen Sabahi (C) demonstrates after a court sentenced deposed president Hosni Mubarak to life in prison at Tahrir Square in Cairo June 2, 2012.Mubarak was sentenced to life in prison on Saturday for ordering the killing of protesters during the uprising that swept him from power last year. REUTERS/Mohammed Salem (EGYPT - Tags: POLITICS CIVIL UNREST TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Zanga-zangar ta dandalin Tahrir dai, na zuwa ne adaidai lokacin da al'umar kasar ke cikin takaicin sakin wasu jami'an ma'aikatar kula da harkokin cikin gida, waɗanda ake shari'arsu tare da tsohon shugaban kasar, dangane da zargin kisan gillar masu juyin juya halin daya hambarar da gwamnatin mubarak. A ranar asabar ce dai Mubarak mai shekaru 84 da haihuwa, da tsohon ministan harkokin cikin gida Habib al-Adly, suka samu hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan wakafi, ayayinda aka saki wasu manyan jami'ai guda shida. Wannan hukunci dai ya samu mummunan martanin adawa daga al'ummar kasar, batu daya jagoranci bazuwar dubban mutane akan tituna tare da kira da ayi adalci. Al'ummar ta Masar dai sun bukaci da a yanke wa Mubarak hukuncin kisa tattare da mukarrabansa dake da hannu a kisan da akayi wa masu juyin juya hali.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita          : Usman Shehu Usman