Libiya: Ko boyayyun gidajen yari nawa ne?
May 22, 2025
Kimanin gidajen yari shida aka gano, wadanda a ka yi amannar cewa mayakan sa-kai na rundunar Tabbatar da Zaman Lafiya ta kasar Libiyan wato Stabilisation Support Apparatus (SSA) da aka kashe jagoranta Abdel Ghani al-Kikli ne ke gudanar da su. An dai samu kimanin gawarwaki 58 da ba a gane ko su wanene ba a gidajen yarin, a yayin da aka balle su tare da sakin mutanen da ke cikinsu da aka jima da ba da sanarwar mutuwarsu ba tare da sanin sun tsare a cikin irin wadannan gidajen yarin ba.
An dai kashe Abdel Ghani al-Kikli a wani dauki-ba-dadi da mayakansa suka yi da dakarun da ke kare gwamnatin hadin kan kasa karkashin jagorancin Firaminista Abdul Hamid Dbeibeh da al'ummomin kasa da kasa suka amince da ita. Musayar wutar ya afku ne, bayan da firaministan ya nemi al-Kikly ya mika ikon sansanonin da ke karkashinsa ga dakarun gwamnatin. Masu lura da abun da ke wakana a Libiya dai, sun yi ammanar cewa gidajen yarin da aka bankado somin tabi ne ta la'akari da yadda kasar ta Libiya ta zama sansanin kungiyoyin mayakan da ke samun tallafi da goyan baya daga 'yan siyasa da masu fasa kwabrin miyagun kwayoyi da fataucin dan Adam da suka fi karfin gwamnatin da ke fama da rarrabuwar kawuna.