1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul a Majalisar Ministocin Masar

July 17, 2011

A gabannin garambawul ɗin shugaban gwamnatin riƙon ƙwaryar Masar zai gudanar a Majalisar ministocinsa, ministocin uku sun yi murabus

Mohamed Al-Orabi tsohon Ministan harkokin wajen MasarHoto: picture alliance/dpa

Ministocin ukku sun yi murabus daga majalisar ministocin Masar daga ciki har da Ministan harkokin wajen ƙasar Mohammed al-Orabi, a gabanin garambawul ɗin da Frime Minista Essam Sharaf ke shirin aiwatarwa a majalisar ministocin na sa. Ana sa ran Sharaf, wanda yake shugabantar gwamnatin riƙon ƙwaryar Masar tun bayan da boren ƙin jinin gwamnati ya kifar da mulkin tsohon shugaba Hosni Mubarak a watan Fabrairu, zai gabatar da sabuwar Majalisa a gobe litini idan Allah ya kai mu bayan ya kammala wani zama na mako guda a birnin Al-ƙahira. Wannan sanarwar ta yin murabus na ministan harkokin wajen wadda aka rawaito ta gidan talabijin na ƙasa, ya zo ne sao'i kaɗan bayan da shugaba Sharaf ya zaɓi Hazem Beblawi wani ƙwararre a fanin tattalin arziƙi da kuma Ali al-Silmi shugaban jamiyyar Wafd na masu ra'ayin sassauci a matsayin mataimakan sa.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Zainab Mohammed Abubakar