1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garambawul ga gwamnatin Japan

August 27, 2007

Praministan ƙasar Japon Shinzo Abbe, yayi garambawul ga gwamnatin sa , a sakamakon mummunan kayin da ya sha a zaɓen yan maljalisun dokokin da ya a ka shirya a watan da ya gabata.

Kazalika Shinzo Abbe, ya gudanar da kwaskwarima ga hukumar zartaswa, ta jam´iyar PLD mai riƙe da ragamar mulki.

A na zargin shugabanin wannan jam´iya da zama ummal ibasar kayin da ta sha a zaɓen ranar 29 ga watan juli da ya wuce.

A sakamakon wannan garambawul, ministan harakokin waje, Taro Aso ya yi murabus inda ya zama saban sakatare Janar na Jam` iyar PLD.

Ya ce ya yanke wannan shawara, da zumar farfaɗo da martabar jam´iyar wacce a halin yanzu, ruwa ya doki babban zakara.

An naɗa Nobutaka Machimura, a matsayin saban ministan harakokin waje.

Shinzo Abbe da ke shan suka daga jama´ar bayan zaɓen, ya yi tsayuwar gwamen jaki, akan kiran da ake masa, na yayi murabus daga muƙamin sa.