Garambuwal a ministocin Nijar
October 20, 2016Sai dai kusoshin tsohuwar gwamnatin sun ci gaba da zama a cikin sabuwar majalisar ministocin, inda alal misali ministan cikin gida Mohamed Bazoum ya ci gaba da kasancewa kan kujerarsa, a yayin da Hassoumi Massaoudou tsohon ministan tsaro ya samu mukamin ministan ma'aikatar kudi ta kasa.
A yayin da ministan kiwon lafiya Kalla Moutari ya maye gurbin Hassoumi Massaoudou a kan harakokin tsaron. Ministan ma'aikatar man fetur Foumakoye Gado ya ci gaba da zama kan mukaminsa. 'Yan adawa shida da suka samu mukami a cikin sabuwar gwamnatin sun hada da Malam Almoustapha Garba da Illiassou Idi Mainassara daga jam'iyyar MNSD Nasara.
Shugabannin jam'iyyun da suka dafawa shugaban kasa a lokacin zaben watan Febrarun da ya gabata, ko wannensu ya ci gaba da zama a cikin sabuwar majalisar ministocin gwamnatin kasar.