Gargaɗin Koriya Ta Arewa ga ƙasashen ƙetare
April 5, 2013Ma'aikatar kula da harkokin tsaron Amirka ta gargaɗi Pyonyang da ta guji abun da ta kira tsokana idan ba haka ba, za ta yi nadama da abun da zai biyo baya. Mai magana da yawun ma'aikatar da ke Pentagon George Little ya ce kamata yayi ƙasar ta bi dokokin ƙasa da ƙasa ta kuma mutunta alƙawuran da ta yi a baya.
Ƙudurorin Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da dama ne suka haramtawa Koriya ta Arewa sarrafa makaman na nukiliya. Pentagon ta ce zata aika da batturan naurorin kakkaɓo makamai masu linzami domin kare sansanoninta da ke da tazarar kusan kilometa dubu uku da ɗari biyar daga Koriya ta Arewar inda take da dakaru dubu shida.
George Little ya kuma kare matakin atisayan da Amurkan ta gudanar da Koriya ta Kudu, wanda ake ganin shine ya fusata Koriya ta Arewa ta shiga yin barazanar ƙaddamar da yaƙi
To sai dai bayan da ta gargaɗi ƙasashen ƙetare da su shirya barin ofisoshin jakadancinsu da ke Pyongyang, Birtaniya ta ce bata da niyyar yin haka cikin gaggawa amma zata tattauna matakin da ya dace a ɗauka tare da ƙawayenta na ƙasa da ƙasa dangane da rikicin da ke neman ritsawa da mashigar ruwan ta Koriya.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Usman Shehu USman