1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Gargadi ga masu yakar juna

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2023

Wakiln Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin Sudan Volker Perthes ya yi gargadi ga bangarorin da ke yakar juna a kasar, yana mai cewa za su iya fuskantar hukunci kan laifukan da suka aikata a fadan da suke yi.

Sudan | Gudun Hijira | Yaki
Dubban mutane ne dai, rikicin na Sudan ya tilasta musu gudun hijira.Hoto: Isaac Mugabi/DW

Volker Perthes ya yi wannan gargadin ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a birnin Brussels na kasar Belgium, inda ya ce yaki tsakanin sojojin gwamnatin juyin mulkin sojan Sudan din da kuma dakarun tawayen RSF da ya shiga makonsa na uku na barazanar zama rikicin kabilanci da kuma ra'ayi ko ma yakin basasa. A cewarsa akwai tarin rahotanni na cin zarafin dan Adam da suka samu, wadanda suka hadar da kisan gilla da fyade da kuma sace kayan jama'a. Perthes ya ce, wadan nan abubuwa, na kara sanya al'ummar Sudan din fatan ganin bayan sojojin da ke yakar juna.