Gargadi kan sabon juyin mulki a Burundi
June 1, 2015Talla
A wata sanarwa da ya fidda dazu, shugaban na Burundi ya ce dukannin wani shiri na kifar da gwamnatinsa ba zai yi tasiri ba, inda ya bukaci 'yan jam'iyyarsa da su sanya idanu don ganin mulki na dimokradiyya a kasar ya cigaba da wanzuwa.
To sai dai duk da wannan kashedi nasa da ma bukatar da ya ce ake da ita ta kare tsarin dimokradiyya a kasar, 'yan dawa da kungiyoyi na fararen hula na cigaba da sukarsa kan abinda suka kira yin karen tsaye ga kundin tsarin mulki ta hanyar neman wani sabon wa'adin mulki da suka ce ya saba ka'ida.