1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garin Bama ya fada hannun 'yan Boko Haram

September 2, 2014

Rahotanni daga garin Bama na jihar Borno a Najeirya na cewa 'yan Boko Haram ne ke iko da garin ko da dai rundunar sojin kasar ta musunta hakan.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Hoto: picture alliance/AP Photo

Mutanen da ke fitowa daga gari Bama sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun karbe iko da garin kuma ana ganin suna yawo a cikin garin da bidigoginsu ba tare da fuskantar wata barazana ba kuma tuni suka fara kafa totocin su a sassan garin. Al'ummar wannan gari da ma wadanda da ke makotaka da shi na ci gaba yin tururuwa suna shiga Maiduguri don tsira da ransu.

A baya dai hedkwatar tsaro Najeriya ta fitar da sanarwa wanda ke nuna cewa sun dakile kokarin ‘yan bindigar kuma ma har sun kashe da dama daga cikinsu tare da yin alwashin cewa ba za su kyale wani bangare na kasar a hannun wasu ba. Sanarwar wacce aka wallafa a shafin Twitter mallakar rundunar tsaron ta kuma ce babu karin bayani kan yawan wadan suka mutu ko suka jikata amma dai daga bangaren jami'an tsaron babu wanda ya samu ko kwarzane.

Sojin Najeriya sun ce har yanzu su ke rike da garin Bama ba 'yan Boko Haram ba.Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

To amma wani mazaunain Maiduguri kusa da tashar Bama ya ce sun ga sojojin a cikin wani hali da suke zaton sun tsere ne daga Bama din kamar yadda ya shaidawa wakilinmu na Gombe Al-Amin Sulaiman Muhammad a wata hira da ya yi da shi ta wayar tarho bisa sharadin ba zai bayyana sunansa ba saboda dalilai na tsaro.

Garin Bama wanda ke da nisan kilomita 80 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno shi ne na baya-bayan nan da ‘yan bindigar suka karbe iko da shi bayan karbe garuruwa da dama a sassan jihar inda suka ayyana daular musulunci a garin Gwoza a makon da ya wuce. Har wa yau a makon na jiya kungiyar Boko Haram ta sake karbe iko da garin Dikwa hedkwtar karamar hukumar Dikwa a jihar Borno inda ta kafa tutocinta tare da nada jagoran da ake kira da Amir wanda zai kula da harkokin gudanarwa a garin.

Wani daga cikin matasan nan da ke aikin sa kai don taimakawa jami'an tsaro wanda aka fi sani da suna Civilian JTF ya shaidawa DW cewa ‘yan bindigar na shirin afkawa Maiduguri nan gaba kadan musamman ganin sun karbe garuruwa da dama daga hannun dakarun Najeriya.

Mawallafi: Al-Amin Sulaiman Muhammad
Edita: Ahmed Salisu/USU