1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karuwar garkuwa da mutane a yankin Sahel

Jean-Marie Magro USU
November 8, 2023

Mutane da yawa a yankin Sahel na fadawa a tsaka mai wuya, suna mutuwa a fadace-fadace. A cewar wani binciken da cibiyar nazarin tsaro ta yi, an yi garkuwa da mutane 180 a Mali da Burkina Faso a farkon rabin shekara.

Hoto: Ben Curtis/picture alliance/AP Photo

A bisa kiyasin wannan cibiyar nazarin harkokin tsaro ko wacce rana ana satar mutum guda a tsakanin Mali ko Burkina Faso. Patrick matashi ne dan shekaru 30, kuma ma'aikacin jinya a wani asibiti mai zaman kansa. Patrick ganau kan irin wannan rayu, inda a misali a watan Juni suna kan titi suna tafiya a tsakiyar Mali sai ga 'yan ta'adda da ke ikirarin jihadi sun dakatar da direba. Daga baya Patrick ya sami labarin cewa an sake shi ne sakamakon musayar da aka yi da mayakan jihadi da aka tsare. Shi dai za a ce ya yi sa'a domin akasarin labari yawanci game da wadanda aka 'yantar da su don fansa da za su kai miliyoyi kudi. Amma da wuya wani iya sanin yawan jama'ar Sahel, wanda ya zuwa yanzu illar garkuwa da muta ne  ta fi shafa: A cewar masaniyar siyasar Bafaransa Flore Berger, wace ke a cibiyar yaki da aikata laifuka da ke a Geneva. A nzahiri dai 'yan tawaye da jami'an tsaron gwamnati suma suna yin garkuwa da mutane a wasu sassan na yankin Sahel, amma galibin 'yan ta'addar masu da'awar jihadi ne ke ke aikata garkuwar kuma a aljihunsu ne akasssarin kudin fansa ke tafiya. Wasu lokutan akwai abin da masu garkuwar ke so fiye da kudi, in ji Flore Berger.

Garkuwa da mutane a yankin Sahel na dada karuwa

Hoto: Souleymane Ag Anara/AFP

A cewar masanan dai dabarar masu garkuwar tana canzawa, idan manufar farko ita ce a mamaye yankin, to ana amfani da garkuwa da mutane don hukunta mutanen da ba su yi biyayya ba. Mataki na biyu shi ne game da tabbatar da iko a kan yankin. Sannan, alal misali, ana tsare ma'aikatan ba da agaji na kasa da kasa akalla tsawon sa'o'i 24. Wannan da dai sauran dabaru masu garkuwa ke amfani da su don tsoratawar da fada ikonsu.