Garkuwa da mutane: Sojojin Najeriya sun bai wa jama'a laifi
March 26, 2024![Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa](https://static.dw.com/image/66424676_800.webp)
Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce ayyuka sun yi wa sojojin Najeriya yawa, abin kuma da ke sanya su dogaro da bayanan na sirii da suke samu daga fararen hula.
Babban hafsan tsaron, Janar Chris Musa, ya bayyana takaicin yadda jama'a ke kwatanta wa sojojin maboyar 'yan bindigar, amma kuma bayanan nasu ke hannu riga da asalin wuraren da suke kasancewa a zahiri.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai rundunar soji a Najeriyar, ta sanar da nasarar ceto daliban makarantar Kuriga su 137 wadanda 'yan bindiga suka sace a jihar Kaduna da ke arewacion kasar.
Ya kuma tabbatar da cewa an gwabza a tsakanin sojojin da 'yan bindigar da suka sace dalibai, kafin aka kai ga kubutar da su, sai dai bai yi bayanin yadda aka samo yaran ba tare da wani ain ya sami ko da daya daga cikin su ba.