1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkuwa da wasu jamusawa biyar a Yemen

Ibrahim SaniDecember 28, 2005

Ana ci gaba da sanin makomar wasu jamusawa biyar da akayi garkuwa dasu a kasar Yemen

Ya zuwa yanzu dai a cewar kamfanin dillancin labaru na AFP, anyi garkuwa da mutane biyar din ne tare da direban su akan hanyar wani gidan cin abinci dake kudancin tashar jiragen ruwa ta garin Aden akan hanyar su ta zuwa birnin Shabwa dake da nisan kilomita 480 daga babban birnin kasar wato Sana´a.

A cewar rahotannin yau kusan kwanaki uku ke nan mutanen da suka aikata wannan danyan aikin ke tsare da Jamusawan guda biyar da suka fito daga gida daya tare da direban nasu guda.

Tuni dai ofishin jakadancin Jamus dake kasar ta Yemen ya tabbatar da bacewar wadannan jamusawan guda biyar ciki har da tsohon Jakadan kasar a kasar Amurka a Lokacin mulkin tsohon Shugaba Gerhard Schroeder,wato Juergen Chrobog.

Duk da cewa ofishin jakadancin kasar na Jamus a Yemen yaki ya fito fili ya bayyana cewa Jamusawan biyar anyi garkuwa dasu ne, tuni gidan talabijin din Ard dake nan Jamus ya tabbatar da cewa Mr Juergen Chrobog da matarsa daya da kuma yayan sa uku anyi garkuwa dasu ne a kasar ta Yemen.

A cewar ma´aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta Yemen tuni aka gano gurin da ake hasashen a nan ne ake tsare da Jamusawan, a don haka tuni yan sanda suka yiwa gurin kawanya tare da gudanar da bincike na kwakwaf.

Bisa dai gamsassun bayanai da suka iso mana daga kasar sun shaidar da cewa yan bindiga dadin da suka fito daga wata kabilar kasar sunyi garkuwa da jamusawan biyar ne don tursasawa gwamnatin kasar sako yan kabilar su da ake tsare dasu.

Da man can a cewar bayanan wasu daga cikin kabilan kasar kanyi garkuwa da yan yawon shakatawa don neman biyan wata bukata tasu a matsayin ban gishiri in baka manda.

Garkuwa da Mr Juergen Chrobog da kuma iyalan nasa hudu tare da direban su daya ya kasance abu na huhu a jerin garkuwa da yan bindiga dadin suka yi a cikin wannan shekara da muke ciki.

Idan dai za a iya tunawa a makon daya gabata sai da akayi garkuwa da wasu yan yawon shakatawa biyu daga kasar Austria, wanda bayan kwanaki uku aka sako su.

A watan nuwamba ma anyi garkuwa da wasu yan kasar Swiss biyu a gabashin kasar to amma su basu dade ba aka sako su.

Bugu da kari an kuma taba yin garkuwa da wasu yan kasar Spain guda guda uku a watan Agusta, to amma a wannan karon a kudancin kasar, wanda bayan yan kwanaki suma aka sako su.

Kusan dai dukkannin mutanen da akayi garkuwa dasu a cikin wannan shekarar ana sako su ba tare da asarar rayuka ba ko kuma jikkata.

Rahotanni dai sun fasalta kasar ta Yemen a matsayin kasa dake a matsayin gida ga kungiyyar Alqeda ta Usama Bin laden,bisa hasashen cewa anan ne kungiyyar ta samo asalin ta.