Garumbawul ga shugabannin sojojin Sudan
February 27, 2018Talla
Shugaba Omar Hassan al-Bashir na Sudan ya fatattaki babban habsan sojojin kasar Lantanar Janar Emadeddin Adawi daga bakin aiki, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar ya ruwaito. Sannan an bayyana sunan Laftanar Janar Kamal Abdul Maaruf a matsayin sabon babban habsa na sojojin kasar.
Kana Shugaba Hassan al-Bashir ya ya yi sauye-sauyen shugabannin sauran hukumomi na tsaron kasar ta Sudan da suka hada da hukumar leken asiri.