1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar ƙwallon ƙafa ta janyo rigima a Masar

February 2, 2012

Fiye da mutane 70 ne suka mutu sanadiyyar wasan ƙwallon ƙafa a Masar

epa03088472 An Egyptian soccer fan runs between empty seats as security forces stand on the pitch at the stadium of Port Said, Egypt, 01 February 2012. According to local media reports, at least seventy people were killed and 200 injured on 01 February when riots broke out following a football match in northern Egypt, according to local media reports. Some of the dead are believed to be security officers. The riots broke out after a game between Egypt's Al-Ahali and Al-Masri teams in Port Said, the Egyptian broadcaster said. EPA/STRINGER
Rikicin daya ɓarke bayan wasa a MasarHoto: picture-alliance/dpa

Aƙalla mutane 74 ne suka mutu kana fiye da 200 kuma suka sami rauni a wannan Larabar, bayan da wasu 'yan kallo suka mamaye filin wasa a wata gasar shiga rukuni na ɗaya da ta gudana a yankin arewacin ƙasar Masar. Ma'abota wasa sun kutsa cikin filin ne bayan da ƙungiyar ƙwallon ƙafar al-Masri da cibiyar ta ke garin Port Said ta yi nasarar cin ƙwallaye ukku da ɗaya akan ƙungiyar dake riƙe da kambin rukunin, wato al-Ahly. Daga cikin waɗanda suka sami raunin dai harda jami'an tsaro.

Sai dai kuma wasu rahotanni na cewar jami'an 'yan sandan kwantar da tarzoma sun ja baya a dai dai lokacin da magoya bayan ƙungiyoyin biyu ke yin taho mu gama da junan su. Ana kuma bayyana lamarin da cewar shi ne mafi munin karawa tsakanin ƙungiyoyin cikin gida a Masar tun cikin shekarun 1990.

A faƙaice dai tashin hankalin ya ƙara rura wutar matsalar tsaron da Masar ke fama da ita a al-Qahira, babban birnin ƙasar. A birnin na al-Qahira ne ma'abota ƙwallon suka cinne wuta a wani gini bayan da alƙalin wasa ya busa wusur na kawo ƙarshen wasan wanda aka buga a garin Port Sa'id. Tashar telebijin ta gwamnatin Masar dai ta ruwaito cewar kimanin mutane 1,000 ne suka sami rauni a yayin da ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Masar ɗin kuwa tace adadin su 248 ne.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohamadou Awal Balarabe