1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Wasanni: Gasar cin kofin CHAN na Afirka

August 4, 2025

An fara gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka, ta 'yan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN karo na takwas da kasashe uku ke daukar bakunci.

Afirka | Gasa | CHAN
'Yan wasan kwallon kafa na Angola, guda cikin kasashe masu masaukin bakiHoto: Daniel Beloumou Olomo/AFP/Getty Images

Kasashen Kenya da Yuganda da Tanzaniya ne, ke karbar bakuncin gasar ta 'yan wasan kwallon kafa da ke bugawa a gida a nahiyar Afirka wato CHAN. Za dai a kammala wannan gasar a ranar 30 ga wannan wata na Agusta da muke ciki, inda kasashen Afirkan 19 da ke harlartar gasar za su fafata a tsakaninsu. Wannan dai shi ne, adadi mafi yawa na masu buga gasar ta CHAN a tarihi. An kasa kasashen rukuni hudu, inda a rukunin A ake da kasashen Kenya da Maroko da Angola da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da kuma Zambiya. A rukunin Ba, akwai Tanzaniya da Madagascar da Mauritaniya da Burkina Faso da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. A rukunin Ca akwai Yuganda da Jamhuriyar Nijar da Guinea da Aljeriya da Afirka ta Kudu, kana kasashen Senegal da Kwango Brazaville da Sudan da Najeriya ke a rukunin Da.

A yayin bude gasar, Tanzaniya guda cikin masu masaukin bakin, ta lallasa Burkina Faso da ci biyu da nema. Ita ma Kenya ta doke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ci daya mai ban haushi, yayin da Maroko ta caskara Angola da ci biyu da nema an kuma tashi wasa tsakanin Madagaska da Mauritaniya canjarsa babu. Jamhuriyar Nijar za ta fafata da Guinea a filin wasa na Nelson Mandela da ke birnin Kampala, yayin da Yuganda mai masukin baki za ta kece raini da Aljeriya. Ita kuwa tawagar Najeriya za ta fafata ne da Senegal mai rike da kofin a halin yanzu a Talatar wannan mako, yayin da Kwango Brazaville za ta kece raini da Sudan. 

An kaddamar da gasar Bundesliga ta 'yan rukuni na biyu a karshen makon da ya gabata, inda tuniaka fara fafatawa tsakanin kungiyoyin da ke neman zama zakara. A wasannin da aka kara a makon farko Shalke O4 ta doke Hertha Berlin da ci biyu da daya, yayin da Darmstadt ta casa Bochum da ci hudu da daya. Karlsruher ta doke Penssen Münster da ci uku da biyu, kana  Paderborn ta yi nasara a kan Holstein Kiel da ci biyu da daya. Elversberg ta doke Nüenberg da ci daya mai ban haushi, haka kuma Arminia Bielefeld ta yi wa Fortuna Düsseldorf kisan mummuke da ci biyar da daya.

Har yanzu muna fagen kwallon kafa, inda a jajibirin fara gasannin lig-lig na Turai hada-hadar cinikayyar 'yan wasa na ci gaba da kankama a tsakannin kungiyoyin kwallo kafa da ke kokarin yin damara domin tunkarar kakar wasa mai zuwa. Tottenham ta Ingila, na zawarcin dan wasan gaba na Real Madrid kuma dan kasar Brazil Rodrygo Silva de Goes domin maye gurbin dan wasanta Son Heung-min mai shekaru 33. Manchester United na kokarin danne Newcastel, wajen cefano dan wasan gaban RB Leipzig ta Jamus Benjamin Sesko. Chelsea ta yi babban kamu na cefano dan wasan baya na Ajax Amsterdam Jorrel Hato a kan fam miliyan 37. A laligar kasar Spain kuwa ana kila wa kala kan yi wa 'yan wasan Barcelona biyar rijista, domin taka wa kungiyar leda a kakar wasa mai zuwa. 'Yan wasan sun hada da Marcus Rashford da Joan Garcia da Roony Bardghji da Wojciech Szczęsny da kuma Gerad Martin. Kungiyar da ke rike da kofin laliga ta ce, tana iya kokari domin bullo wa wannan lamari kafin karshen wannan mako.

Bai wa matasa kuzari ta hanyar wasan kwallon Kwando a Gabon

03:31

This browser does not support the video element.

Tawagar 'yan matan Najeriya ta lashe kofin gasar kwalon kwando ta nahiyar Afirka, wadda aka kammala a birnin Abidjan fadar gwamnatin Cote d'Ivoire. A wasan karshe da aka fafata a Lahadi uku ga wannan wata na Agusta da muke ciki, 'yan matan na Najeriya sun tumurmusa takwarorinsu na Mali da ci 78 da 64. Wannan nasara da tawagar 'yan matan Najeriya ta samu na zama cikon wasanni 29 na kwallon kwando da take bugawa a nahiyar Afirka ba tare da an doke ta ba, tun bayan rashin nasara da ta yi a birnin Yaounde na Kamaru a wasan neman matsayi na uku na gasar cin kofin Afirka a watan Oktoban 2015.