1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamerun: Gasar iya sarrafa burodin gargajiya a Yaounde

April 29, 2026

A birnin Yaounde, an gudanar da gasar fidda gwanin iya sarrafa burodin gargajiya ta hanyar yin amfani da albarkatun noma na cikin gida dangin su Rogo da Masara da Dankali da Ayaba da dai sauransu

Symbolbild  | Sinsheim 2024 | Mann klaut Bäckereiwagen
Hoto: Viktor Gladkov/Zoonar/picture alliance

An shirya wannan gasa ce da nufin karfafa yin amfani da garin da ake samar wa ta hanyar wadannan albarkatu da ake nomawa a cikin gida da kuma bunkasa zaburar da matsa wajen kafa kananan masana'antu.

Matasa sama da 20 ne suka baje baiwa da basira a wannan gasa da aka shirya da nufin karfafa yin amfani da garin da ake samarwa a cikin gida da kuma zaburar da masu jin jini a jika wajen kafa masana'antun sarrafa burodi na gargajiya. A lokacin gasar da ke zama karon farko, kanshin ya turike birnin Yaoude, inda aka baje kolin nau'i-nau'i na burodi da dangoginsa irin su Kek ko biskit da aka sarrafa da garin albarkatun noma dangin su Rogo da Masara da Dankali da Doya da kuma Ayaba a maimakon garin alkama. Wannan guda ne daga cikin wadanda suka shirya gasar.

''Muna fatan dorewar irin wadannan ranaku na baje kolin kayyakin cikin gida, domin wayar da kan jama'a da kuma hukumomi kan ingancin nau'ikan gari na cikin gida da kuma yadda ake sarrafa su. Da akwai mutane da dama da suka jajirce a wannan fanni kuma wannan dama ce da za su nuna irin kwarewa da basirar da suke da ita wajen sarrafawa da kuma yin amfani da nau'ikan gari na cikin gida da kuma rage dogaro da garin da ake shigowa da shi daga waje.''

Hoto: Krupetskiy/Depositphotos/IMAGO

Karin bayani: Fafaroma Leo na tattaunawa da Kiristoci a Kamaru

Hakazalika gasar ta birnin Yaounde ta kasance wata kafa ta karin ilimi da bude kwakwalawar mahalartan, inda suka kara fahimtar sabbin dabarun sarrafa garin cikin ciga tare da ingantashi wajen samar da burodi da dangoginsa cikin salo da hikima injin wannan matashiya.

"Na koyi yadda ake yin burodi da nau'ikan gari iri-irin namu na cikin gida, abin da a can baya ban iya ba. Yanzu na koyi karin dabarun yadda ake sarrafa wadannan nau'ikan gari ta yadda zan inganta amfanin da nake yi da su tun da farko.''

Karin bayani: 'Yan Kamaru 16 da ke wa Rasha yaki sun mutu a Ukraine 

Bumbin jama'a da suka halarci baje kolin, sun samu damar dandana nau'ikan kayayyaki da aka sarrafa, lamarin da ya ja hankalin da dama daga cikin su musamman ma inganci da dadin dandano da kuma lafiyar da ke tattare da na'ukan abincin, lamarin da zai kara karkato hankalin su zuwa abincin da ake sarrafa a gida Kamaru.

''Wannan nau'ikan abinci na da matukar kyau da kuma muhimmanci ga lafiya, sannan suna taimakawa wajen wajen yakar wasu cutuka saboda ba sa kunshe da wadansu sinadarai.''

Hoto: Charlotte Orr/The Picture Pantry/picture alliance

Karin bayani: Batun nada mataimakin shugaban kasa ya janyo cece-kuce a Kamaru 

A karshe dai mahalarta gasar sun bayyana aniyar ci gaba da jarircewa domin bunkasa wannan sana'a, tare da yin alkawarin bude cibiyoyin samar da kayayyakin da ake sarrafawa da garin cikin gida a sassa daban-daban na kasar. Sai dai hanzari ba gudu ba, rashin isassun kayan aiki na zamani na iya hana ruwa gudu.

Amma duk da haka, tuni aka fara samun bullar sabbin masu rungumar sana'ar sarrafa garin cikin gida a Kamaru, inda suke samar wa jama'a da burodi dan gida mai inganci a kuma farashi mai sauki.

 

 

 

 

 

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani