1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Jamus ta gaza a FIFA Club World Cup

Lateefa Mustapha Ja'afar MA
July 7, 2025

An yi waje road da kungiyoyin Jamus, a gasar kungiyoyin kwallon kafa na duniya wato FIFA Club world Cup. An sabunta kwamitin koli na Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Jamhuriyar Nijar, Novak Djokovic ya sake lashe wasansa.

FIFA Club World Cup | 2025 | Real Madrid | Borussia Dortmund
Borussia Dortmund ta sha kashi a hannun Real Madrid Hoto: Adam Hunger/AP/picture alliance

A karshen mako kungiyoyin kwallon kafa na Bayern Munich da takwararta Borussia Dortmund sun gaza kai bantensu, bayan da suka sha kashi a gasar kungiyoyin kwallon kafa na duniya wato FIFA Club World Cup a wasannin dab da na kusa da na karshe wato quarter finals. Tun da fari dai sai da kungiyar kwallon kafa ta SE Palmeiras SP ta Italiya ta kwashi kashinta a hannun Chelsea ta Ingila da ci biyu da daya, kana PSG ta Faransa ta caskara Bayern Munich ta Jamus da ci biyu da nema. Daga bisani ita ma Borussia Dortmund ta Jamus, ta sha kashi a hannun Real Madrid ta Spaniya da ci uku da biyu.

Jamal Musiala zai jima yana jinya, sakamakon karaya da gocewar kashi da ya samu a kafarsa dayaHoto: Malachi Gabriel/ZUMA/picture alliance

Mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Jamus Julian Nagelsmann ya nuna damuwarsa kan yadda fitaccen matashin dan wasan Jamus din kana dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Jamal Musiala ya samu rauni, tare kuma da yi masa jaje da fatan samun lafiya. Mai shekaru 22 a duniya Musiala  ya samu karaya a kwabrinsa da kuma gocewar kashinsa na agara duk a kafa guda, a yayin fafatwarsu da kungiyar kwallon kafa ta PSG ta Faransa a gasar cin kofin kwallon kafa na kungiyoyin kwallon kafa na duniya wato FIFA Club World Cup a karshen mako. Musiala ya samu raunin a daidai lokacin da suke shirin fafatawa a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya wato World Cup da za a yi a badi. Tuni dai cikin wata sanarwa Nagelsmann ya bayyana cewa, Musiala ba zai iya buga wasannin da Jamus za ta yi nan gaba cikin wannan shekarar ba.

Bankwana da gawar Diogo JotaHoto: Manu Fernandez/AP Photo/picture alliance

A karshen mako aka gudanar da jana'izar dan wasan Liverpool Diogo Jota da kaninsa Andre Silva a yankin Gondomar da ke kusa da birnin Porto na kasar Portugal. Shugaban kasar Portugal Marcelo Rebelo de Sousa da firaministansa Luis Montenegro sun samu halartar jana'izar dan wasan na Liverpool. Jota da kaninsa Silva sun rasa rayukansu ne sakamakon hadari mota da ya rutsa da su a Spaniya, biyo bayan fashewar da tayar motarsu ta yi. Matar Jota da 'yan uwansa na daga cikin dandazon mutanen da suka halarci jana'izar, ciki kuwa har da tawagar 'yan wasan Liverpool da wasu abokan marigayin daga Manchester United da Manchester City har ma da sauran kungiyoyi.

Novak Djokovic na ci gaba da nuna kwarewa a kwallon TennisHoto: Al Bello/Getty Images

Shahararren dan wasan kwallon Tennis na duniya da ya lashe gasar har sau bakwai Novak Djokovic ya lashe wasansa na 100, a gasar Tennis ta duniya wato Wimbledon. Djokovic ya ci gaba da kafa tarihi a gasar kwallon Tennis a duniya, inda a karshen mako ya sake kafa wani tarihin bayan da ya lallasa abokin karawarsa a zagaye na uku na gasar ta Wimbledon Miomir Kecmanovic da ci shida da uku da shida da nema da kuma shida da hudu. Da wannan nasara da ya yi, Djokovic ya shiga cikin jerin manyan jadawali guda biyu. Jannik Sinner da ke a matsayi na farko a jadawalin na Tennis kuwa, ya ci gaba da nuna kwarewa a kokarin ganin ya lashe gasar All England Club.

Jannik Sinner yayin da ya lashe gasar ATP World Tour a baraHoto: Antonio Calanni/AP/picture alliance

Shi kuwa shararren dan wasan kwallon Tennis na Amurka da ke a matsayi na biyar a jadawalin kwallon Tennis din Taylor Fritz ta fadi masa gasasshiya ne, bayan da ya samu nasarar zuwa wasan dab da na kusa da na karshe wato quarter-final a karo na uku a gasar ta Wimbledon ba tare da wani tarnaki mai yawa ba. A zagaye na hudu na fafatarwarsu da abokin karawarsa Jordan Thompson na Australiya ne, Thompson din ya nemi fita daga gasar sakamakon raunin da ya samu a cinya. Da ma dai tun da fari, Fritz  din ya samu nasara a kan Thompson da ci shida da daya da kuma uku da nema. Ba'amurken mai shekaru 27 a duniya Fritz da ya samu nasarar zuwa wasan karshe na Grand Slam a gasar U.S. Open a bara, na ci gaba da kokarin tabbatuwar mafarkin Amurka na samun dan wasan Tennis namiji da zai lashe gasar Wimbledon bayan Pete Sampras a shekara ta 2000.

Carlos Alcaraz na fatan kare kambunsaHoto: Corinne Dubreuil/abaca/IMAGO

Mai rike da kambun gasar ta Wimbledon Carlos Alcaraz ya sha da kyar, a kokarinsa na kare kambunsa. A fafatawarsu da dan kasar Rasha Andrey Rublev dan kasar Spaniyan mai shekaru 22 a duniya, Alcaraz ya lallasa dan Rublev da ke matsayi na 14 a jadawalin kwararrun 'yan wasan Tennis din a duniya da ci shida da bakwai da shida da uku da shida da hudu da kuma shida da hudu. A yanzu dan wasan da ke matsayi na biyu a jadawalin Tennis din, Alcaraz zai fafata da Cameron Norrie na Birtaniya a wasan dab da na kusa da na karshe wato  quarter-finals.

Aryna Sabalenka na kokarin lashe gasar WimbledonHoto: Asanka Brendon Ratnayak/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa Aryna Sabalenka da ke matsayi na farko a jadawalin kwararrun 'yan wasan Tennis mata a duniya, na kara nuna karfin kwanjinta ne bayan da ta samu nasarar kai wa ga wasan na dab da na kusa da na karshe wato quarter-finals. Sabalenka ta lallasa Emma Raducanu kana ta samu nasarar a kan Elise Mertens da ci shida da hudu da bakwai da shida a wani wasa da aka gwada karfin kwanji. A hannun guda kuma na'urar shata layi ta janyo mayar da zafafan martani, bayan da tangardar da ta fuskanta ta hana Anastasia Pavlyuchenkova samun maki a wasan da ta samun nasara a kan 'yar kasar Birtaniya Sonay Kartal. Koda yake duk da matsalar da aka samu ta yi nasarar kai wa ga wasan dab da na kusa da na karshe wato quarter-finals a karo na biyu a gasar ta Wimbledon, bayan ta lallasa Kartal din da ci bakwai da shida da shida da hudu.

Mathieu van der Poel dan tseren keke dan kasar HollandHoto: George Deswijzen/PRO SHOTS/picture alliance

Dan kasar Netherlands Mathieu van der Poel ya lashe zagaye na biyu na gasar tseren keke ta Tour de France, inda ya kammala a gaban dan kasar Sloveniya Tadej Pogacar. 'Yan tsere da dama sun yi tuki kan-kan-kan, abin da ya sanya a karshe dukan su suka fara fafutukar ganin sun cimma burinsu na lashe gasar. Van der Poel ya zo na daya da taki guda kana Pogacar ya biyo bayansa a matsayi na biyu, yayin da dan kasar Denmark Jonas Vingegaard ya kammala tseren a maatsayi na uku.