1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Gasar kokawar gargajiya a Nijar

January 2, 2024

An kammala gasar kokawar gargajiya ta neman lashe takobi da aka saba yi a duk shekara a Jamhuriyar Nijar. An gudanar da gasar ne a birnin Agadez, inda gwani na ganayen wasan ya lashe takobi.

Issaka Issaka, zakarar gasar kokawa a Jamhuriyar Nijar
Gwanin kokawar gargajiya a Nijar, Issaka IssakaHoto: Gazali Abdou Tasawa/DW

A makon jya ne aka kawo karshen gasar kokawa neman takobi a karo na 44  a garin Agadez na Jamhuriyar Nijar inda gwanin kokawa a jihar Dosso Kadri Abdou wanda aka fi sani da sunan Issaka Issaka ya yi nasarar samun takobi a karo na 6 a jere. Da hakan dai Issaka Issaka ya kafa tarihi a fannin kokawar gargajiya a kasar ta Nijar.

Garin Dosso ya rikide da sowa a lokacin da Issaka Issaka ya yi nasarar kayar da dan kokawar jihar Maradi Mati Souley, inda ‘yan asalin mahaifar tasa suka yi ta bayyana farin ciki da samun wannan galaba ta tarihi.

Daga yankin Gaya ma haka lamarin murnan ya kasance inda rawa da annashuwa da kuma ba da kyaututukan murnar dai ba ta misaltuwa.

A cewar Assamaou Moumouni bayan kafa tarihi da ya yi, Issaka Issaka ya fitar da yan Dosso kunya.

To sai dai ganin irin yadda ya zama zakaran gasar kokawar ta gargajiya sau da dama, ya sanya wasu ke ganin bai kamata ya kara samun gurbi ba, lamarin da ya sa al'ummar Dosso suka mika kira zuwa ga sauran ‘yan kasar Nijar a kan dauwamar da hadin kai a tsakanin 'yan kasa.

Rabon yankin Dosso da samun takobin dai tun a shekara ta 1975 a zamanin Salma dan Rani, kuma Kadri Abdou wato Issaka Issaka ya zama dan kokowar da ya kafa tarihin cin takobi har sau shida kuma sau uku a jere kuma a cewarsa yana godiya ga masoyansa kana ‘yan Dosso su kwantar da hankalinsu.