1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin farko na wasan kusa da karshe

Mouhamadou Awal Balarabe
May 9, 2022

A karshen mako aka gudanar da matakin farko na wasan kusa da karshe na neman kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar Afirka.

 Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahly ta Masar
Kungiyar kwallon kafa ta Al-Ahly ta MasarHoto: Giuseppe Cacace/AFP

 Laya ta yi Al Ahly ta Masar da ke rike da kofin kyaun rufi sakamakon cin kaca 4-0 da ta yi wa ES Setif ta Aljeriya. Abu daya ne zai iya hana Al Ahly kaiwa wasan karshe na kofin zakarun Afirka, illa Setif ta doke da ci biyar ba tare da ta zura ko da kwallon daya ba.
A nata bangaren kuwa Wydad Casablanca ta bi Petro Atletico ta Angola har gida Luanda kuma ta doketa da ci 3-1. Kungiyoyin hudu za su gudanar da mataki na biyu na wasan nasu ne a karshen mako mai zuwa. Ita dai Petro ba ta da wani fatan samun nasara, duk da neman cika burin zama kungiyar Angola ta farko da ta kai wasan karshe na champions lig.

A kofin confederation kuwa, kwallon da John Bakata ya zira a ragar RS Berkane ta Maroko bayan karin lokaci ya bai wa TP Mazembe ta Dimukradiyyar Kwango damar lashe matakin farko na wasan kusa da na karshe na gasar a ranar Lahadi a Lubumbashi. Ita ma Orlando Pirates ta Afirka ta kudu ta samu nasara a kan al Ahly ta Tripolin Libiya da ci 2-0.


A Jamhuriyar Nijar, a wannan Litinin aka shiga kwana na uku na wasannin tankade da rairaya na neman tikitin zuwa gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta 'yan kasa da shekaru 20 da za ta gudana a kasar Masar a 2023. Wasannin wadanda suka hada kasashe bakwai na Afirka ta Yamma na rukunin B da kuma ke gudana a karkashin sabon tsarin da hukumar CAF ta fito da shi, zai bayar da damar fitar da kasashen da za su wakilici yankin a gasar ta Masar.

A nan Jamus, an gudanar da wasannin makon kusa da na karshe na kakar wasannin 2021-2022, ranar da ta bai wa Leverkusen damar shiga gasar cin kofin zakarun Turai sakamakon lallasa TSG Hoffenheim da ta yi da ci 4-2. Wannan yana nufin cewa ta bi sahun Bayern Munich da Borussia Dortmund wadanda suka cancanta tun tsawon makonnin da suka gabata, biyo bayan tabbacin da Leverkusen ke da shi na kammala Bundesliga a matsayi na 3. Tuni ma Bayer Leverkusen ta inganta matsayinta idan aka kwatanta da kakar wasa ta bara, inda ta kammala a matsayi na 6. Ko da koci Gerardo Seoane na kungiyar, sai da ya ce laya ta yi wa 'yan wasansa kyau rufi a bana.

Bundesliga: FC Bayern München da Borussia DortmundHoto: Stuart Franklin/Getty Images

 

Yakin neman matsayi na 4 tsakanin RB Leipzig da SC Freiburg na ci gaba da yin zafi. Sai dai ‘yan wasan Domenico Tedesco na Leipzig sun yi nasara doke FC Augsburg da ci 4-0, ciki har da kwallaye biyu da Christopher Nkunku ya zura. Wannan ya sa RB ci gaba da yi wa Freiburg tazarar maki biyu duk da doke Union Berlin da ta yi da 4-1.  RB Leipiz na bukatar yin kunnen doki kawai a mako mai zuwa don samun tikitin shiga gasar Europa Lig. 

A dangane da tikitin karshe na gasar cin kofin Europa kuwa, za a nemi gwanin ne tsakanin Union Berlin, mai matsayi na 6, da FC Cologne da ke a matsayi na 7 bayan da ta doke Wolfsburg da ci 1-0 a ranar Asabar.

VfL Wolfsburg da FC Union BerlinHoto: Swen Pförtner/dpa/picture alliance

A kasan teburin Bundesliga kuwa, VfB Stuttgart ta samu karin maki daya wanda ya zame masa tamkar dubu da ta tashi 2-2 da zakarar kwallon kafar Jamus Bayern Munich. Don haka kungiyar za ta ci gaba da fafutuka a mako mai zuwa don ganin cewa ba ta ganganra karamin lig ba.

Ga koci Pellegrino Matarazzo, wannan muhimmiyar nasara ta samu ne ta hanyar aiki tukuru.

"A cikin satin, na nuna wa 'yan wasana fannonin da Bayern Munich ke da rauni domin in kara musu kwarin gwiwa. Mun san cewa Bayaern za ta jera 'yan wasan da ta fi ji da su, domin gabatar da sabon kambunsu a ciikin kyawawan hali. Mun fara wasan da kyau, inda muka fara zura kwallo a raga, amma don samun nasara a kan wannan kungiya ta Bayern Munich, dole ne mun nuna kwarewa sosai. Duk da kalubale, 'yan wasan sun nuna bajinta, za mu iya yin nasara a mako mai zuwa. Muna fata za ta wadatar wajen dawwama a babban lig."

Pellegrino Matarazzo mai horar da 'yan wasan StuttgartHoto: Matthias Hangst/Getty Images

Idan Stuttgart na son dawowa a matsayi na 15 a mako mai zuwa, dole ne ta yi nasara a wasa da FC Cologne, kuma ta yi fatan a doke Hertha Berlin a garin Dortmund. Idan kuwa hakarta ba ta cimma ruwa ba, to ita Stuttgart na da tabbacin buga wasannin tankade da rairaya na kasancewa a babban lig din kwallon kafar Jamus.

Matashin dan wasan tennis nan na kasar Sipaniya Carlos Alcaraz ya lashe muhimmiyar gasa a Madrid, da ke zama kambu na biyu a gasar Masters,  ta hanyar murkushe lamba 3 na duniya kuma mai rike da kofin Alexander Zverev da ci 6-3 da 6-1 a cikin mintuna 62. Alcaraz ya cimma burinsa ne bayan kawar da manyan dawan fagen tennis daya bayan daya, ciki har da Rafael Nadal, da kuma gwani na gwanayen duniya Novak Djokovic, lamarin da a taba ganin irinsa ba. Alcaraz ya zama dan tennis mafi karancin shekaru da ya yi nasarar doke su a gasa duka. 

Dan wasan Tennis na Spain, Carlos AlcarazHoto: Manu Fernandez/AP/picture alliance

A wannan litinin Carlos Alcaraz ya hau matsayi na shida a teburin tennis na duniya, kwanaki hudu kacal bayan ya cika shekaru 19 da haihuwa. A halin yanzu dai yana da kofunan biyar, ciki har da na Masters 1000 guda biyu bayan nasarar da ya samu a Miami a farkon Afrilu. Shi ne mafi karancin shekaru da ya kai wannan jimillar kofunan tun bayan Rafael Nadal a 2005 a lokacin da yake da shekara 18.

A fagen damben boxing, Saul "Canelo" Alvarez dan kasar Mexico wanda ya canza aji ya dibi kashinsa a hannun Dmitry Bivol na Rasha, lamarin da ya kai alkalan yanke shawara dakatar da wasan kafin ya zo karshe a birnin Las Vegas na Amirka. Wannan dai shi ne karo na biyu da canelo ya barar da dambe tun bayan rungumar boxing a rayuwarsa, lamarin da Bivol na Rasha ci gaba da rike kambunsa na ajin matsakaicin nauyi na WBA.