1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gasar wasannin Olympics 2021

July 23, 2021

Shirye shirye sun kankama na bude gasar wasannin Olympics a birnin Tokyo a yanayi na dokar kulle saboda annobar corona.

Olympische Sommerspiele 2020 | Rudern | Nazanin Malaei, Iran
Hoto: Laurent Gillieron/KEYSTONE/picture alliance

A wannan Juma'ar ce ake bude gasar wasannin Olympics na bana a birnin Tokyo na kasar Japan. Bikin bude gasar zai sami halartar manyan baki 950 ne kawai saboda annobar Corona.

Wasannin za su gudana a yanayi na dokar ta baci da aka sanya karo na hudu a yankin Tokyo baki daya saboda yaduwar corona.

Firaministan Japan Yoshihide Suga na fatan wasannin na Olympics da za a yi ba tare da yan kallo ba za su gudana cikin nasara duk da yanayin da ake ciki na annoba.