A shirin na wannan makon mun tabka muhawara a tsakanin Muhammad Rabiu Dantine wanda aka fi sani da Young Ustaz a shafukan sada zumunta da ke da ra’ayin a soke lefe a kasar Hausa da kuma Farida Haske, matashiya a Kano da ke adawa da dokar da ta haramta lefe a jihar Kano.