Ci gaba da sauya shekar gwamnoni da manyan ‘yan siyasa zuwa jam’iyyar APC mai mulki na jawo muhawara a faɗin Najeriya.Shin wannan alamar ƙarfi ce ga siyasa ko kuma barazana ga dimokuradiyya? A cikin shirinmu na Gaskiyar Magana, za ku ji fahimtar Dr. Bashir Ibrahim Kurfi, masanin siyasa da Ibrahim Abdullahi Waiya, kwamishinan yaɗa labarai na Kano.