Gawar Fafaroma Francis ta isa cocin St Peter domin ban-kwana
April 23, 2025
Gawar Fafaroma Francis ta isa cocin St. Peter's Basilica bisa rakiyar manyan limaman darikar Katolika, inda kiristoci mabiya za su yi ta'aziyyarsu ta karshe kafin jana'izarsa da za a gudanar a ranar Asabar, wacce za ta samu halartar shugabannin kasashen duniya da dama. Sai dai sabanin yadda al'ada cocin ta tanada, an kwantar da gawar shugaban darikar katolika ta duniya a kasa kamar ya bukata, inda ya yi fatan samun jana'iza mafi sauki.
Karin bayani: Akwai fata kan samun Fafaroma daga Afirka
Ana sa ran dubun-dubatar mutane ne za su karrama Fafaroma Francis a tsawon kwanaki uku, kamar yadda ya faru lokacin jana'izar Fafaroma Benedict XVI a 2022, inda mutane 200,000 suka yi ban kwana da shi kafin a binne shi. Sai dai domin tinkarar kwararar al'umma, hukumomi sun tanadi mataki shingen karfe na hana zirga-zirgar maziyarta, da kara yawan motocin bas da ke hidima a fadar Vatican, da kuma karfafa matakan tsaro a kofofin shiga dandalin St. Peter.
Karin bayani: Fafaroma ya rasu bayan ya yi fama da doguwar jinya
Kamar yadda ya faru a shekarar 2005 a lokacin jana'izar John Paul II, da dama daga cikin shugabannin kasashe da sarakuna za su halarci jana'izar shugaban cocin Katolika, wanda zai gudana cikin tsauraran matakan tsaro a ranar Asabar.