1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gawar Mandela ta shiga kabari

December 15, 2013

An binne tsohon Shugaban Afirka ta Kudu Marigayi Nelson Mandela, a garin Kunu da ke Lardin Gabashin Cape.

Hoto: Reuters

Marigayi Mandela tsohon jagoran gwagwarmaya da mulkin nuna wariyar launin fata, ya bar duniya yana da shekaru 95 da haihuwa bayan doguwar jinya. Akwai dubban mutane suka halarci zana'idar, wadda aka fara da kai gawar zuwa zauren taro, inda sojoji suka yi mata rakiya.

Jikar marigayin Nandi Mandela ta yi jawabi a madadin iyalan:

"Mun yi rashin kaka, mun yi rashin muyar ka da ke tsawatar mana idan muka yi abin da ya saba. Mun rasa muryarka da ke shaida mana rayuwarka. Mun rasa dariyarka."

Shugaban kasar ta Afirka ta Kudu ya ce, rayuwar Marigayi Mandela za ta ci gaba da kasancewa cikin zukatan 'yan kasar:

Hoto: picture-alliance/dpa

"Yau aka kawo karshe wata gagarumar tafiya wadda aka fara shekaru 95 da suka gabata. Shi ne karshen shkearu 95 masu matukar tasiri da nasara na gwarzon kwaton 'yanci, wanda ya mika wuya domin aiki wa mutanen Afirka ta Kudu."

Firimnistan kasar Habasha Hailemariam Desalegn na cikin wadanda suka gudanar da jawabi, wanda yake rike da jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka. Inda ya ce, gwagwarmayar da Mandela, bangare ne kan kawar da mulkin mallaka da sauran danniya a kan mutanen Afirka.

Shugabar Malawi Joyce Banda ta gudanar jawabi a madadin shugabannin kasashen kudancin Afirka, wadda ta ce, saboda nuna hali irin na Marigayi Mandela, ya kai ta yafe wa mutanen da suka yi yunkurin hana mata samun mulki.

Shugaban Tanzaniya Jakaya Kikwete ya yi jawabi, musamman saboda yadda kasarsa ta bayar da mafaka wa 'yan gwagwarmayar Afirka ta Kudu lokacin gwamnatin mulkin nuna wariyar launin fata. Kikwete ya tunatar da masu addu'ar zana'idar yadda tsohon jagoran 'yan gwagwarmayar Marigayi Mandela, ya sulale zuwa Tanzaniya daga bisani ya wuce zuwa biranen Lagos na Najeriya da Accra na kasar Ghana, domin neman taimakon fara amfani da karfi domin kawar da gwamnatin nuna wariyar launin fata.

Akwai wasu shugabannin da tsaffin shugabannin kasashen da suka halartar zana'idar ta girmamawa.

Hoto: DW/S. Govender

Sojoji suka yi rakiya wa gawar Nelson Marigayi Mandela zuwa kushewa da kade-kaden da rera taken kasar.

Jiragen sama masu saukan ungulu na sojoji Afirka ta Kudu sun yi shawagi kasa-kasa dauke da tutocin kasar, yayin da ake binne Mandela a kabari.

Gwagwarmayar neman kawo karshen gwamnatin wariyar nuna launin fata ta Turawa tsiraru, a farko lokacin da aka fara abu ne mai matukar wuya, kuma damar samun nasara kalilan ce, amma saboda tsayuwar daka daga karshe wannan nasara ta tabbata.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh