1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Gawar Raila Odinga ta isa mahaifarsa

October 18, 2025

Madugun adawar Kenyan ya rasu ne ya na da shekara 80 kuma ya jima yana gwagwarmayar neman shugabancin kasar.

Ana yi wa Odinga wanda ya rasu yana da shekara 80 kallon jagoran gwagwarmaya da inganta dimokuradiyyar kasar ta gabashin Afirka
Ana yi wa Odinga wanda ya rasu yana da shekara 80 kallon jagoran gwagwarmaya da inganta dimokuradiyyar kasar ta gabashin AfirkaHoto: Andrew Kasuku/AP Photo/picture alliance

A yau Asabar ce gawar fitaccen magudun adawar nan na Kenya Raila Odinga, ta isa filin wasa da ke yankinsa na yammacin Kenya ta jirgin sama mai saukar ungulu.

Dubban mutane sun hallara a filin domin ganin jagoran gwagwarmayar a karon karshe da kuma yi masa bankwana.

Turmutsutsi wajen karrama gawar Odinga

‘Yan jaridar AFP sun ruwaito cewa tun kafin isowar gawar tasa, aka fara samun alamun hatsaniya yayin da masu zaman makoki suka karya shingen tsaro da aka saka a filin wasan sannan suka haura ta katanga suka shige ciki.

Raila Odinga dai dan siyasar Kenya ne mai matukar farin jini tsakanin 'yan kasar kuma ya shafe dogon lokaci ya na neman shugabancin Kenya.

Kenya: Wacce rawa Raila Odinga ya taka?

Ana yi wa Odinga wanda ya rasu yana da shekara 80 kallon jagoran gwagwarmaya da inganta dimokuradiyyar kasar ta gabashin Afirka.