1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Muatane dubu 50 sun tsere

Abdourahamane Hassane
November 9, 2023

A Gaza mutane dubu 50 sun tsere daidai lokacin da a Faransa aka soma gudanar da wani taro da ke tattauna samar da hanyoyin isar da kayan agaji a yankin zirin Gaza.

Hoto: Hatem Moussa/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin Israila ba ta tura wakili ba a taron da ake gudanarwa a fadar gwamnatin Elysee a karkashin jagorancin shugaban Faransa  Emmanuel Macron. Amma Macron din ya  ce ya tattauna da firaministan israila Benjamin Netanyahu  ta wayar tarho da kuma  shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi, da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, wadanda kasashensu ke taka muhimmiyar rawa wajen isar da kayan agaji zuwa zirin Gazar. A halin da ake ciki kuma kakakin rundunar sojin Istraila Daniel Hagari ya ce za a bude hanyar agajin jin kai a yau domin baiwa al ummar Gaza damar tserewa zuwa yankin kudanci, tuni da wasu dubu 50 suka arce.Red Cross ta damu da kashe-kashen kananan yara a Gaza