Gaza: Israila ta hallaka kwamandan Hamas
November 12, 2018Talla
Sojin Israila sun hallaka wani babban kwamandan Hamas tare da wasu yayan kungiyar su biyar yayin wani farmaki da suka kaddamar a yankin zirin Gaza a ranar Lahadi.
Rahotanni sun ce wani sojin Israila daya ya rasa ransa yayin da rikici tsakanin bangarorin biyu ke neman kara ta'azzara.
Hamas ta ce sojin kundunbala na Israila sun kutsa kai yankin na zirin Gaza kusa da Khan Yunus inda suka harbe Nour Baraka mukaddashin kwamnadan dakarun kungiyar.
A cikin wata sanarwa Hamas ta ci alwashin daukar fansa lamarin da ya sojin Israilar kaddamar da wasu hare hare ta sama.
Ministan tsaron Israila Avidgor Lieberman ya gudanar da taro da manyan hafsoshin sojin kasar domin nazarin yanayin da ake ciki na tsaro.