1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Masar da Qatar na neman a tsawaita batun tsagaita wuta

November 30, 2023

Kasashen Masar da Qatar na shawarwarin neman yadda za a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza da ma batun da ya shafi sakin karin fursunoni.

Hoto: Said Khatib/AFP

Kasashen na Masar da Qatar wadanda ke shiga tsakani a rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas, har ila yau suna kokari kan bukatar kara shigar da kayayyakin jinkai a Zirin na Gaza, kamar yadda kafar yada labarai mallakin kasar Masar ke ruwaitowa a ranar Alhamis.

Kokarin kasashen na Masar da Qatar ya biyo karin wa'adin tsagaita wutar na yini guda da zai cika kwanaki bakwai a gobe Juma'a da aka cimma.

Tsawaitawar da aka yi a yau zuwa gobe Juma'ar ta hada da sakin Isra'ilawa 10 daga hannun Hamas yayin kuma da Isra'ila daga nata bangare za ta saki Falasdinawa fursunoni 30 da take tsare da su.

Masar dai ta ce za ta ci gaba da tsayuwa musamman kan abin da ya shafi ci gaba da shigar da kayayyaki na jinkai zuwa yankunan kudu da ma arewacin Zirin Gaza.