1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaYankin Falasdinu da aka Mamaye

Sake bude mashigar Rafah zai taimaki Gaza?

Mahmud Yaya Azare LMJ
February 2, 2026

Bayan fiye da shekaru biyu da rufe mashigar ta Rafah da ke zama hanya daya tilo da mazauna Zirin Gaza ke iya fita da shiga, Isra'ila ta lamuncewa mazauna yankin fara zirga-zirga ta mashigin da ke kan iyaka da Gazan.

Isra'ila | Zirin Gaza | Falasdinu | Mashigar Rafah | Falasdinawa | Masar
Falasdinawa na jira a tantance su a mashigar RafahHoto: Ramadan Abed/REUTERS

To sai dai irin sharuddan da Isra'ilan ta sanya kafin bude mashigar, ka iya janyo tarnaki ga ayyukan shige da fice na mutane a Zirin na Gaza, inda rahotanni daga kan iyakar ta Rafah ke nuni da cewa ba a tantance ko mutum daya ba balle mutane su fita har zuwa tsakiyar ranar Litinin biyu ga watan Fabarairun 2026 da aka fara amfani da damar bude ta.

Zaman jiran kila wa kala

Duk da cewa an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza har yanzu Isra’ila na ci gaba da kai farmaki, inda rahotanni ke nuni da cewa daga watan Oktobar bara kawo yanzu mutane 509 ne suka halaka yayin da wasu sama da 1,400 suka jikkata. A cewar ma’aikatar lafiya ta yankin, majinyata 20,000 ne ke jiran shiga Masar domin neman magani, yayin da 440 ke cikin halin rai-kwakwai mutu-kwakwai kana akwai masu cutarsankara wato cancer 4,000 da yara kanana 4,500.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

02:06

This browser does not support the video element.

Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross ta nunar da cewa, babu dalilin kirkirar sabon bincike kan majinyatan da ke shirin fita bayan  tuntuni jami'an lafiya da na tsaron sun gama tantanc esu. Wani magidanci da ke fama da cutar sankara wato cancer dansa kuma ke bukatar aikin cire alburusai a kwankwaso, ya nuna takaicinsa ga irin nawar da ake samu wajen ba su dammar ficewa.

Shin mazauna Gaza za su samu damar fita?

Dama dai kungiyar Hamas ta jima da nuna fargabarta kan cewa, Isra'ila za ta iya amfani da batun bude iyakar ta Rafah ba don sahalewa mazauna a Gaza ba sai dai domin ta wulakantasu da sake tursasa musu saboda ka da su yi sha'awar komawa idan suka samu damar fita. Tuni dai Masar ta ce, ta ware asibitoci 300 da likitoci 12,000 da za su tarbi dubban mazauna Gazan da ke shirin shiga kasar su yi jinya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani