1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Yarima ben Salmane ya yi tir da hare-haren Isra'ila

November 10, 2023

Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed ben Salmane ya yi tir da luguden wutar da dakarun Isra'ila ke ci gaba da yi wa zirin Gaza tare da kisan Falasdiwa fararen hula da ba ji ba su gani ba.

Yarima Salmane ya yi tir da hare-hare Isra'ila a Gaza
Yarima Salmane ya yi tir da hare-hare Isra'ila a GazaHoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

Yariman da ke zama shugaban masarautar Saudiyya ya yi wannan furici ne a jajibirin buda taron kasashen Larabawa da Musulmi wanda za a buda a birnin Riyad a ranar Asabar (11.11.2023).

Karin bayani:  Zirin Gaza: Goyon baya daga Larabawa 

A jawabinsa na farko a bainar jama'a kan rikicin na Gaza yarima ben Salmane ya ce suna Allah wadai da cin zarafin fararen hula da kuma keta dokokin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da sojojin mamaya na Isra'ila ke yi.

Karin bayani:   Isra'ila da Saudiyya na daf da dinkewa

Yariman ya kuma jaddada bukatar kawo karshen wannan yaki da tilasta wa al'ummar Gaza tserewa daga matsugunensu da kuma samar da yanayin da ya dace don dawo da kwanciyar hankali da samar da zaman lafiya.