SiyasaJamus
Gbagbo zai iya komawa gida - Ouattara
April 7, 2021Talla
Shugaba Ouattara ya ce Gbagbo da na hannun damansa Charles Ble Goude na da damar komawa kasar ta Ivory Coast a duk lokacin da suka shirya. Furucin shugaban na zuwa ne mako guda bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC ta wanke su daga mumunar rikicin bayan zabe da ya jefa kasar da ke yammacin Afirka cikin wani hali a shekarar 2010 zuwa 2011.
Fiye da mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu a wani rikicin bayan zabe a shekarar 2010 a lokacin da Gbagbo ya ki sauka daga kan karagar mulki duk da shan kaye da ya yi a zaben kasar.