1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Amirka za su tarwatsa masu zanga zanga

May 31, 2020

Zanga-zangar kisan mutumin nan bakar fata na ci gaba da barkewa da daukar sabon salo a Amirka.

Weißes Haus PK US-Präsident Trump makes announcement about China at the White House in Washington
Hoto: Reuters/J. Ernst

Birnin Minneapolis, inda a nan ne ake zargin dan sanda farar fata ya kashe George Floyd  ya shiga  zanga-zanga. 

Biranen Atlanta da Philadelphia da Los Angeles tuni suka sanya dokar hana fita don gudun kada zanga-zangar da mutane ke yi ta rikide ta koma tashin hankali. A birnin Minneapolis 'yan sanda sun gurfanar da wasu mutum 13 da suka keta dokar hana fita suka fito zanga-zanga. Magajin Garin New York Bill de Blasio ya yi kira ga masu zanga-zangar da cewa su kwantar da hankalinsu, mahukumta sun fahimci abin da suke son ganin anyi.

''Mun ji bukatunku a kan ganin an inganta alaka a tsakanin al'umma da 'yan sanda da kuma bukatar yin adalci, kuma kuna son ganin sauyi a cikin al'umma. Mun ji sosai kuma mun fahimce ku. Muna godiya ga masu zanga-zangar lumana. Amma yanzu loakci ya yi da kowa zai koma gida ya huta.'' inji Bill de Blasio


Shugaban Amirka Donald Trump dai ya ce idan har mutane suka ci gaba da fitowa kan tituna a kan kisan wannan bakar fata, to gwamnati za ta duba yiwuwar amfani da sojoji domin tarwatsa su.