131210 Mitchell Nahost
December 13, 2010Gwamnatin Amurka na ƙoƙarin ganin cewa ƙasashen Isra'ila da Falasɗinu sun shiga wani zagaye na tattaunawa dangane da muhimman batutuwan da ke kawo rikici a yankunan. Ministar harkokin wajen Amurkan, Hillary Clinton wadda ta yi wannan maganan ta ce ya kamata a fara yarjejeniya dangane da shata iyakokin Isra'ila da Falasɗinu, a kuma tattauna al'amuran tsaro da tsarin raba ruwan sha, baƙin hauren Falasɗinu da makomar birinin Ƙudus.
Hukumomin Falasɗinu sun nuna takaicin su da shakkar su dangane da makomar tattaunawar sulhu a yankin Gabas ta Tsakiya bayan da gwamnatin Amurka ta kasa cimma sabuwar yarjejeniyar tsawaita wa'adin dakatar da gine-ginen Isra'ila a gaɓar tekun Jordan. A wani jawabin da ta yi, sakatariyar harkokin wajen Amurika Hillary Clinton ta ce duk da cewa Amurka ta kasa tsawaita wa'adin dakatar da gine-ginen, amma za ta ci-gaba da bai wa ɓangarorin biyu ƙarfin guiwa domin shawo kan sauran muhimman matsalolin yankin.
To sai dai, masu sharhi da masu shiga tsakani a yarjejeniyar a ɓangaren Falasɗinu sun ce wannan ya nuna gazawa a ɓangarern Amurka, kuma hakan na nuni da cewa babu tabbacin cimma wata matsaya a yarjejeniyar Yankin Gabas ta Tsakiya nan ba da daɗewa ba.
Mrs Clinton dai ta ce a yanzu haka, za su ci-gaba da tattaunawa wadda ba ta gaba da gaba ba, kuma Amurka za ta ba da shawarwari yadda ɓangarorin za su sulhunta. Ko da yake Ghassen Khatib jami´in yaɗa labarai na hukumar Falasɗinawa, ya ce tattaunawar da ba ta ƙeƙe da ƙeƙe ba, ba za ta yi tasiri ba.
"Abun takaici ne ganin cewa yunƙurin da Amurka ta yi wajen shawo kan Isra'ila ta daina gine-ginen ya ci tura, domin ɓangaren Falasɗinawa sun sha alwashin cewa dakatar da gine-ginen yana ɗaya daga cikin muhimman buƙatun da za su tabbatar da sahihiyar tattaunawar da za ta kawo sulhu a yankin."
A karon farko bayan watanni huɗu, ana sa ran manzon Amurka a Yankin Gabas ta Tsakiya George Mitchell zai koma Isra'ila domin ya ci-gaba da ƙoƙarin samar da yarjejeniya tsakanin Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Mahmud Abbas na Falasɗinu, inda zai fara da halartar taron kwamitin tattaunawar sulhu na ƙasashen Larabawa a birnin Aƙahira a gobe Talata.
A ɓangaren Isra'ila, hukumomin ƙasar na cewa ba za su ƙaddamar da tattaunawa tsakanin wani ƙayyadadden lokaci ba amma Firaminista Netanyahu zai cigaba da tattaunawa ta yadda duk shawarar da aka yanke ba za ta zama barazana ga makomar Isra'ila ba. Mataimakin Firaminista Silva Shalom ya yi ƙarin bayani game da wannan matsayi.
"Amurka ta amince da abun da na yi ta faɗa ne na tsawon shekara ɗaya yanzu. Tsawaita wa'adin dakatar da gine-gine a gaɓar tekun Jordan ba shi da wani muhimmanci wajen cimma wata yarjejeniya. Tambayar dai ita ce ko a shirye Falasɗinawa suke su hau teburin shawara."
A ganawar da Netanyahu ya kan yi da majalisar ministocin sa a kowane mako, bai bayyana komai dangane da batun wannan tattaunawar sulhun ba. Ko da yake, ministan tsaron ƙasar Ehud Barak a wani taron da suka yi da Mrs Clinton, ya ce nan ba da daɗewa ba, za'a raba birnin Ƙudus tsakanin Isra'ila da Falasɗinu. Tuni dai ofishin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa inda ya yi bayanin cewa kalaman ministan tsaron ra'ayinsa ne ba na gwamantin Isra'ila gaba ɗaya ba.
Mawallafa: Sebastian Engelbrecht/Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal