1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Yanayi

Illar sauyin yanayi ga dausayi a Ghana

Rahmatu Abubakar Mahmud LMJ
December 7, 2021

Ghana na daf da yin asarar daukacin dausayinta guda biyar ciki har da na Sakumo, wanda aka ce yana cikin yanayi mafi muni. Masu nazari na bukatar a maido da haramtattun al'adu domin tsare wurare masu danshin ruwa.

Global Ideas Accra in Ghana
Sauyin yanayi na yin illa ga dausayi a kasar GhanaHoto: DW/Ernest Kodjo Ayikpah

Mazauna karamar hukumar Ketu ta Kudu na ci gaba da kokawa kan yadda ambaliyar ruwa ta afku a baya-bayan nan. Bala'in dai na daya daga cikin barnar da aka yi a tafkin Keta, wanda kuma ya kasance dausayi. Yadda yanayin sauran dausayin kasar guda hudu suka kasance wato Densu da Songnor da Muni Pomadze da kuma Sakumo. Sai dai gurbatar yanayi da mamaya da kiwo da bunkasa masana'antu da karuwar jama'a da rashin bin doka, sun karya manufar wadannan muhimman wurare. A cewar wani bincike da aka gudanar tsakanin shekarar 1980 zuwa 2006, wasu ciyayi da ke tsira a cikin guraben dausayi a duniya sun ragu saboda ayyukan mutane a wuraren dausayin.

Matsalar dai ba a Ghana kadai ta tsaya ba, yawancin wuraren dausayi a yammacin Afirka na fuskantar barazana, kuma masu ruwa da tsaki na nuna damuwa da abin da wannan ke nufi ga yankin. Duk kokarin da kasashen duniya keyi don kiyaye yanayin zafi zuwa kasa da digiri biyu a ma'aunin Celcius, an yi imanin ingantaccen hadin gwiwa zai taimaka wajen magance matsalar. Masana kimiyya da masana muhalli sun gano kalubalen da mutum zai iya fuskanta tare da asarar dimbin halittu da muhallin duniya, domin haka suka sanya wasu wurare a matsayin wadanda aka kebe da ake kira dausayi. Dausayi na daya daga cikin wuraren da ake fuskantar barazana a yau, suna zama garkuwa da samar da iska mai tsanani da ambaliya.