Ghana da Mali za su yaki matsalar tsaro a kasashensu
January 17, 2025A wata ganawa da suka yi a birnin Accra na kasar Ghana, shugabannin biyu sun sha alwashin aiki tukuru domin kawo karshen barazanar tsaro da ke karuwa, musamman ta yankin arewacin Ghana da kasashe makwabta irinsu Togo da Benin.
A taron manema labarai, bayan ganawarsa da janar Maiga na Mali, Shugaba John Mahama ya ce batun tsaro manufa ce ta bai daya ga kasashen kuma dole ne su yi aiki tare domin yakiar ayyukan ta'addanci.
Shugaban na Ghana ya kuma amince da kawancen kasashen Sahel na AES da Buirkina Faso da Mali da Nijar suka yi bayan ficewarsu daga kungiyar ECOWAS ta yankin yammacin Afirka.
Kazalika ya kara da cewar duk da koma bayan da suka samu taficewar wadannan kasashen dole ne mu ci gaba da kawancensu, kuma Ghana na goyon bayan Mali.
Karin Bayani:ECOWAS ta sahale wa Nijar da Mali da Burkina Faso fita daga kungiyar